Dakile Hare-Haren ‘Yan Bindiga: Mutane 5 Sun Rasa Rayukansu a Jahar Kaduna

 

Rundunar sojojin ƙasa ta Operation Save Haven ta samu nasarar dakile hare-haren yan bindiga da dama a Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Yace aƙalla mutum 5 cikinsu harda yaro ɗan shekara 10 sun rasa rayuwarsu sanadiyyar harin

Kaduna – Akalla mutum biyar cikinsu harda karamin yaro ɗan shekara 10 suka rasa rayuwarsu yayin harin yan bindiga a yankin karamar hukumar Zangon Kataf, jahar Kaduna, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Wasu da dama sun jikkata a wani harin yan bindiga yayin da sojojin Operation Safe Haven suka fatattaki wasu hari a jahar Kaduna.

Wannan ya biyo bayan sojoji sun dakile yunkurin wasu yan fashi na sace mutun biyu tare da kuɓutar da wasu shida a wurare daban-daban a karamar hukumar Jema’a, kamar yadda.

Wane mataki gwamnati ta ɗauka?

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da kai hare-haren a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Kwamishinan ya gargaɗi nutanen dake yankunan da lamarin ya faru cewa su zauna lafiya, kada su ɗauki doka a hannunsu.

Kwamishinan yace:

“Gwamnatin Kaduna na kara jan hankalin mutane su zauna lafiya su dakatar da tada rikici a tsakaninsu bayan mun samu rahoto daga jami’an tsaro cewa an kashe mutum 5 a wasu hare-hare da aka kai karamar hukumar Zangon Kataf.”

“Rahoton ya nuna cewa an kashe karamin yaro ɗan shekara 10 a dajin Madauchi yayin da yake kiwon dabbobi, an gano gawar yaron kuma an birne ta.”

“Hakanan kuma an kai wani hari Kurmin Masara kusa da Bakin Kogi, inda wani mutumi, Philip Magu, ya rasa ransa kafin daga bisani haɗakar dakarun soji da yan sanda su fatattaki maharan.”

Yan bindiga sun sake kai wani hari na daban

Kwamishina Aruwan ya kara da cewa wasu yan bindiga sun sake kai hari kauyen Jankasa dake yankin karamar hukumar Zangon Kataf.

Aruwan yace dakarun sojoji sun samu nasarar dakile harin duk da cewa an harbe wani mutumi mai suna Haruna har lahira. Hakazalika sojoji sun sake dakile wani harin yan bindiga a yankin Unguwar Rana bayan dogon musayar wuta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here