Cutar Kwalara ta Hallaka Mutane 60 a Jahar Katsina

 

Cutar amai da gudawa wacce aka fi sani da kwalara ta hallaka aƙalla mutum 60 a jahar Katsina.

Kwamishinan lafiya na jahar, Yakubu Nuhu Danja, shine ya bayyana haka a wurin taron kungiyar likitoci.

Danja yace gwamnati ta ɗauki duk wasu matakai da ya kamata domin magance yaɗuwar cutar.

Katsina – Akalla mutun 60 ne suka rasa rayuwarsu a faɗin kauyukan jahar Katsina bayan ɓarkewar cutar kwalara a jahar, Kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jahar, Yakubu Nuhu Danja, shine ya bayyana haka a wurin taron shekara-shekara na ƙungiyar likitoci (NMA).

Sai dai kwamishinan bai bayyana lokacin da suka ɗauki wannan kididdigar rasa rayukan ba, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Wane mataki aka ɗauka bayan ɓarkewar cutar?

Danja ya bayyana cewa a halin yanzun gwamnati na duba dukkan wasu hanyoyin da za’a bi domin dakile yaɗuwar cutar a faɗin kananan hukumomin jahar 34.

Ya kuma kara da cewa gwamnati ta siyo magunguna domin rabawa dukkanin asibitocin dake faɗin jahar.

Kwamishina Danja yace:

“Muna sane da ɓarkewar cutar amai da gudawa a wasu kauyuka jahar mu, gwamnati na iyakar bakin kokarinta wajen dakile cigaba da yaɗuwar cutar.”

“Gwamnati ta tanadi dukkan magungunan da zata yaki cutar domin raba su ga dukanin asibitocin jahar.”

“A halin yanzun akwai mutum 1,400 da suka kamu da cutar ta amai da gudawa yayin da 60 daga cikinsu suka mutu. Ina amfani da wannan dama wajen kira ga Katsinawa cewa cutar kwalara abun gudu ce.”

Tsaftar muhalli da abinci

Kwamshinan lafiya ya kara da gargaɗin Katsinawa da su tabbatar da suna tsaftace mahallin da suke rayuwa a ciki, wanke hannu lokaci bayan lokaci, da wanke kayan itatuwa kafin su ci.

Danja ya gargaɗi masu aikin abinci tun daga mata da sauransu da su tabbatar da suna kulle abincinsu domin magance shigar kwayar cuta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here