Kungiyar Tuntuba ta Arewa ta Koka Kan Yadda Gwamnati Ke Tafiya Kan Fannin Tsaro

 

Kungiyar tuntuba ta Arewa ta ce shugaba Buhari ya kasance abin kunya ga ‘yan Arewa.

Kungiyar ta bayyana haka ne yayin da ta ke koka yadda gwamnatin ke tafiya ta fannin tsaro.

Kungiyar ta kuma bayyana yadda tuntuni take nuni da cewa, gwamnatin ta gaza wajen magance matsalolin tsaro.

Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta bayyana shugaba Buhari a matsayin abin kunya ga Arewa, kasancewar ya gagara komai kan matsalar tsaro da kasar ke fuskanta, musamman arewacin Najeriya.

Mr. Emmanuel Yawe, sakataren yada labarai na kungiyar ne ya bayyana haka yayin wata hira da jaridar Daily Sun da aka wallafa ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, inda ya ke mamakin yadda shugaban ya kasance tsohon soja amma ya kasa tabuka wania abin kirki.

Mr. Emmanuel ya bayyana yadda kungiyar ta ACF ke nuna damuwarta game da yadda kasar nan ke ciki, yana mai cewa, Arewa ta kasance cikin firgici, sannan babu zaman lafiya.

Yayin da aka tambaye shi irin damuwar da ACF ke ciki game da yawaitar tashe-tashen hankula a Arewa, Mr. Emmanuel ya ce:

“Ka san muna matukar nuna damuwa game da yanayin tsaro a kasar fiye da kima yayin da mutumin da yake shugaban kasa ba kawai janar ne na yaki kadai ba, tsohon Shugaba ne na mulkin Soja a baya.

“Ta yaya za ka ba da shawara ga gwamnatin da wani mutum ke jagoranta wanda yake da tsohon tarihin aikin tsaro?

“Wasu daga cikin mu da suka taka rawar gani a lokacin da ya hau kan karagar mulki a shekarar 2015 mun ji cewa abin da ke faruwa a halin yanzu ya kai abin kunya matuka.”

ACF ta jima da gane Najeriya na cikin mummunan hali

Da yake sake jaddada yadda matsalolin kasar ke kara hauhawa, Mr Emmanuel ya ce, ACF ta jima tana fadin cewa, halin da Najeriya ke ciki na muni ya ta’azzara.

A kalamansa kamar yadda yazo a Daily Sun, cewa ya yi:

“Mun fada da babbar murya cewa yanayin tsaro ya munana. Mun fadi hakan, ba a boye ba cewa ‘yan Najeriya musamman ‘yan Arewa ba su da kwanciyar hankali. Abin da ya kamata a yi shi ne siyasa ta shawo kan lamarin.

“Abin takaici, gwamnatocin jahohi da na tarayya, sun gaza a kan wannan. Duk mun san akwai wata hadaka da ta mamaye kungiyoyin farar hula, sojoji, majalisa da zartarwa wadanda basa son ganin karshen wannan rashin tsaro.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here