Yajin Aikin Ma’aikatan Lafiya: Mutune 620 Sun Mutu a Mozambique

 

Aƙalla mutum 620 sun rasa rayukansu a cikin kwanaki 40 da suka gabata sakamakon yajin aikin da ma’aikatan lafiya a Maputo, babban birnin Mozambique ke yi.

Wannan ne karon farko a tarihin ƙasar da likitoci suka haɗa kai wajen gudanar da yajin aikin, inda suka zaɓi tsawaita zanga-zanga na tsawon kwanaki 21 duk da barazar kisa da aka yi musu.

Sai dai likitocin sun yi alkawarin bai wa marasa lafiya kula da ƙankanin lokaci don rage musu raɗaɗin da suke ciki.

Ma’aikatan lafiyar sun ce sun shiga yajin aikin ne saboda ba su da magunguna da kayan aiki masu mahimmanci – sun ce ta kai ga su ke biya daga aljihunsu don tara motocin ɗaukar marasa lafiya da kayan masarufi.

Cikin buƙatu da suka nema har da son tsige ministan lafiya Armindo Tiago.

Sai dai gwamnatin ƙasar ta bayyana nadama kan matakin da likitocin suka ɗauka na tsawaita yajin aikin da suke yi, duk da cewa ta ce an samu gagarumin ci gaba wajen magance korafe-korafensu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com