Oyo: An Kama Wasu Mutane Akan Babbakke Naman ‘Yan Sanda
Ana zargin wasu mutane biyu da cin babbakakken naman yan sanda a Ibadan babban birnin jihar Oyo.
Duka su biyun sun karyata zargin yayin da kowa yake alakanta laifin ga dan uwansa.
‘Yan sandan dai an girke su ranar 22 ga Oktoba don kula da masu zanga zangar #endsars lokacin da suka gamu da ajalinsu.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Oyo ta tabbatar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da cin naman ‘yan sandan da aka kona lokacin zanga zangar EndSARS.
Read Also:
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da kama wanda ake zargin ranar Asabar a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN).
Wanda ake zargin, wata mata mai shekara 34 da kuma wani dattijo mai shekaru 43, an mika su ga cibiyar bincike ta ‘Force Intelligence Bureau’ a hedikwatar hukumar da ke Abuja don fadada bincike, a cewar sa.
Yar shekara 34, an zarge ta da cin sassan daya daga cikin yan sanda da aka kona, lamarin da ta karya duk da tana wajen da abun ya faru, ta ce dayan da ake zargi dai ya bata wasu sassa ta ajiye masa.
Dan shekara 43, shima bai karyata kasancewar sa a wajen da abin ya faru ba, amma yace matar ce ta dauki wasu sassa kuma ta roki ya bata tsumman da zata daure a ciki.
‘Yan sandan dai an girke su ne don kula da kula da masu zanga zangar EndSARS ranar 22 ga Oktoba lokacin da suka gamu da ajalinsu.