Mutane 14 Sun Mutu a Harin ‘Yan Bindiga a Jahar Kaduna
Wasu yan bindiga sun sake kai hari Kudancin Kaduna, inda suka kashe akalla mutum 14 tare da kone wasu gidaje.
A wani harin ɗaukar fansa, wasu mutane sun kona wata Rugar Fulani baki ɗaya.
Kakakin yan sandan Kaduna, ASP Jalige, ya tabbatar da kai harin biyu, yace mutane su daina ɗaukar doka a hannun su.
Kaduna – Akalla mutum 14 suka rasa rayukansu a wani sabon hari da yan bindiga suka kai kauyen Mado, karamar hukumar Zangon Kataf, jahar Kaduna.
Maharan sun kone wasu gidaje da dama yayin da suka kai harin ranar Asabar da daddare.
Da yake zantawa da Dailytrust, shugaban kwamitin tsaro na yankin Aytap, Mista John Bala Gora, ya yi mamakin yawaitar hare-haren duk da kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya.
Gora ya sake kira ga jami’an tsaro su kara zage dantse wajen kare al’umma da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.
An kona rugar fulani
Read Also:
A wani harin daukar fansa, wasu mutane sun kone wata rugar fulani a Kankada, yankin Madakiya, karamar hukumar Zangon Kataf da sanyin safiyar Lahadi.
Daya daga cikin mazaunan rugar da aka taba, Halima Haruna, wacce aka kubutar kuma aka kaita caji ofis na Zonkwa, tace maharan sun zagaye rugarsu da safiyar Lahadi.
Matar shugaban fulanin Kankada, Haruna, tace ta ga gawar mutum biyu, mace da namiji, yayin da take neman wurin ɓuya, kamar yadda vanguard ta rawaito.
Tace:
“Dole ta sa muka gudu muka ɓuya yayin da wasu daga cikin mutanen rugar suka tsere cikin jeji domin ceton rayuwarsu.”
“Bamu san meyafaru da su ba yanzun, mun shafe awa 3 kafin jami’an tsaro su zo su ɗauke mu zuwa caji ofis ɗin Zonkwa. Sun kone mana gidajen mu baki ɗaya.”
“Maharan sun faɗa mana sun zo ɗaukar fansa ne kan harin da aka kai musi ranar Asabar da daddare, wanda mu bamu san komai ba.”
Hukumar yan sanda ta tabbatar Da yake tabbatar da harin guda biyu, Kakakin rundunar yan sandan jahar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, yace an tura jami’an yan sanda yankunan da abun ya shafa.
Ya yi kira ga mutanen Zangon Kataf, da kuma kudancin Kaduna baki ɗaya, su daina ɗaukar doka a hannun su.