Kisan Gilla: Gwamna Simon Lalong ya Nemi Yafiyar Al’ummar Ondo da Jos

 

Gwamnan jahar Filato, Simon Lalong, ya roki gwmanati da al’ummar Ondo yafiya kan kisan da ya faru a Jos .

Gwamnan yace waɗanda suka aikata lamarin sun yi hakane domin wargaza zaman lafiyar da aka gina a jahar.

Shugaban Fulani, Kabir Muhammed, yace sun hakura domin zaman lafiyar Najeriya.

Plateau – Gwamna Simon Lalong na jihar Filato, ya roki gwamnati da kuma al’ummar jahar Ondo yafiya bayan kisan gillan da aka yiwa mutanensu a Jos, kamar yadda premium times ta rawaito.

Legit.ng Hausa ta rawaito muku cewa a ranar 14 ga watan Agusta aka kashe matafiya 23 yan jahar Ondo yayin da hanya ta biyo da su Jos.

Hakanan kuma yayin lamarin, an jikkata wasu mutum 23 daga cikin matafiyan, waɗanda suka dawo daga wa’azin da suka halarta a Bauchi.

Tawagar gwamnatin Filato ta je ta’aziyya Ondo

Gwamna Lalong ya nemi yafiya kan harin ta bakin mataimakinsa, Sonny Tyoden, wanda ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa Ondo yin ta’aziyya, kamar yadda punch ta rawaito.

Mr Tyoden yace sun kawo wannan ziyarar ne domin yin ta’aziyya da kuma neman afuwar gwamnati da mutanen Filato daga iyalan mamatan da kuma al’ummar Ondo baki ɗaya.

Mataimakin gwamnan ya nemi yafiya kan kisan da wasu bara gurbi suka aikata, inda yace yan ta’addan sun yi haka ne don kashin kansu ba domin addini ba ko kabila.

Mista Tyoden yace:

“Gwamna Lalong ya damu matuka da faruwar lamarin, wanda aka aikata da nufin tada rikici domin wargaza zaman lafiyar da aka samu a jahar tun zuwan shi Ofis shekara 6 da suka gabata.”

Gwamnatin Filato ta ɗauki matakin da ya dace

A jawabinsa, gwamnan jahar Ondo, Akeredolu, ya yabawa gwamna Lalong bisa gaggauta ɗaukar matakai don magance abinda ka iya zuwa ya dawo.

Gwamnan wanda mataikinsa, Lucky Aiyedatiwa, ya wakilata yace gwamnan na samun labarin ya yi gaggawar zuwa kasuwar shanu domin jajantawa shugabannin Fulani.

Fulani sun hakura da abunda ya faru Shugaban Fulani na yankin kudu maso yamma, Kabiru Muhammed, yace sun yafe abinda ya faru domin tabbatar zaman lafiya a Najeriya.

Ya yi alkawarin cewa babu wani harin ɗaukar fansa da za’a kai domim zaman lafiyar Najeriya ta fi bukatar ɗai-daikun mutane.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here