kwalara: Mutane 2,791 a Najeriya Sun Rasa Rayukansu
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya, NCDC ta ce cutar amai da gudawa ta kashe mutun 2,791 a jahohi 28 da kuma Birnin Tarayya Abuja, daga farkon shekara zuwa yanzu.
Rahoton na NCDC ta fitar a ranar Talata na cewa mutun 81,413 ne suka kamu da cutar ta kwalara daga watan Janairu zuwa yanzu.
Read Also:
Daga cikin jahohin da lamarin ya shafa akwai Adamawa da Bauchi da Bayelsa da Benue da Borno da Cross River da Delta da Ekiti da Enugu da kuma babban birnin Najeriyar wato Abuja.
Sauran sun hada da Gombe da Jigawa da Kaduna da Kano da Katsina da Kebbi da Kogi da Kwara da Nasarawa da Niger da Ogun da Osun da Plateau da Sokoto da Taraba da Yobe da Rivers da kuma jahar Zamfara.
Rahoton ya kuma ce yara ‘yan shekaru daga biyar zuwa 14 ne cutar ta fi addaba.
Kazalika an samu raba dai-dai na kashi 50-50 na jinsin maza da na mata da cutar kwalarar ta kama.