Anyi wa Mutane Miliyan 36 Rijistar Jam’iyyar APC a Fadin kasar nan – Gwamna Badaru
Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya tabbatar da cewa za a yi taron jam’iyyar APC a watan Yuni
Kamar yadda ya sanar da manema labarai, kwamitin rikon kwaryan ya shirya tsaf don sauke nauyin dake kansu
Gwamnan yace a halin yanzu anyi wa mutane miliyan 36 rijistar jam’iyyar APC a fadin kasar nan
Gwamnan jihar Jigawa kuma shugaban kwamitin tsari na jam’iyyar APC, Badaru Abubakar, yace za a yi gagarumin taron jami’iyyar a watan Yuni.
Daily Trust ta ruwaito cewa, akwai rade-radin dake yawo na cewa za a kara wa’adin mulkin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a matsayin shugaban kwamitin tsari na jam’iyyar kuma za a kara lokacin taron ya wuce watan Yuni.
Read Also:
Amma a wata tattaunawa da manema labarai a sakateriyar jam’iyyar APC da yayi a ranar Talata, Badaru yace kwamitin rikon kwaryan ya shirya domin sauke nauyin dake kansu.
“Tabbas za a yi. Na san kwamitin riko kwaryan ya shirya zuwa watan Yuni kuma za mu goya musu baya tare da yin duk abinda ya dace domin ganin cewa mun sauke nauyin dake kanmu zuwa watan Yuni,” yace.
Badaru yace APC ta yi wa mambobi miliyan 36 rijista a wannan sabunta rijistar ‘ya’yan jam’iyyar da take yi kuma za a kammala zuwa ranar 31 ga watan Maris.
“Da farko mun buga na mambobi dubu goma sha biyu, amma yanzu haka mun wuce miliyan goma, mun kai miliyan 36. Hakan ba dole ya isa ba.
“A yanzu, muna cigaba da bugawa saboda idan mutane suna ganin ayyukan da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi fiye da mulkin da ya gabata, sai goyon bayan ya karu,” yace.