Mutum Mai Taimakon Al’Umma: Hanyar da ya bi da Kuma Abinda ya Samar
“Tarbiyya ta na farawa daga gida” sun ce, amma akwai abubuwa tattare da ita.
Ka da ka yi tunani kawai, aiwatar. Mafificin Mutum mai taimakon al’umma shi ne wanda ya ke duban kura-kurai da matsaloli; ya duba abubuwan da su ka haddasa su, ya yi ƙoƙarin kawar da munanan abubuwa har inda su ke.
Mafifitan mutane a cikinmu su ne waɗanda gabaɗaya su ke gamsar da mutanen da su ke ƙoƙari da gano tayadda za su aiwatar.
Su ne waɗanda su ke kallon buƙatun sauran mutane su kuma sadaukar da kansu a kansu.
Su ne waɗanda su ka yi imani kan yin amfani da ɗan abin da ke hannunsu domin su biyawa sauran al’umma buƙatunsu.
Babu wata mafificiyar hanya ga mutum wacce zai maida kansa abin da ba ya mutuwa sama da wannan abu guda ɗaya na yin wani aiki domin al’umma a madadin ya yi domin kansa kaɗai. Wannan kuma gabaɗaya aiki ne a aikace da ya ke wakiltar faɗin: Albert Pike; “Duk abin da mu ka yi wa kanmu kaɗai zai mutu ne tare da mu, amma abin da mu ka yi ga sauran al’umma da ma duniya zai cigaba da kasancewa kuma ba ya mutuwa,”.
Malam Kashifu Inuwa ya yi tafiya zuwa ganawa da ƙungiyoyin ba da agaji na duniya domin buƙatar al’ummarsa (ƴan Nageriya) da ma dukkan al’umma baƙaƙen fata gabaɗaya.
Read Also:
Na samu damar shaida ganawa daban-daban da ya yi da gidauniyar ƙasar Qatar, tare da neman tallafin haɗin gwiwar aiki tare domin biyan buƙatun mutanensa (ƴan Nageriya) waɗanda su ke da ƙaramin ƙarfi su ke kuma buƙatar agajin ƙungiyoyin taimako na duniya.
A wannan rana, mafarkinsa ya zama gaskiya ta hanyar kira da ba da kykkyawan sakamako wanda ya sanya farin ciki da jindaɗi a cikin zukatan al’umma da kafatanin baƙaƙen fata.
Malam Kashifu ya samar da ƙarfin gwiwa, aminci da farin ciki a rayuwar al’umma ta hanyar ayyukansa na jinƙai dalilin haɗin gwiwa da gidauniyar ƙasar Qatar wajen aiwatar da ayyukansa na jinƙai da taimakon al’umma.
Wani zai iya cewa Kashifu ɗan aiken Allah ne kamar yadda mu ke da Annabi Isah ɗan Nana Maryamu wanda ya kasance ɗan aiken Allah da bayyana Mu’ujizozi. Wannan ba wai ina kamanta cewa matsayinsa ɗaya da Annabi Isah ko Allah ba, amma dai ina nuna cewa Allah ne ya turo shi domin mutane da dama.
Tare da tasirinsa, mutane masu lalurar gani sun amfana ta hanyar aikin tiyatar ido kyauta, an raba kekuna masu ƙafa uku ga mutane masu buƙata ta musamman, mutane masu ƙaramin ƙarfi sun samu abin biyan buƙatun rayuwa ta hanyar ba su abin dogaro da kai, marasa aikin yi an ba su kayan aikin noma da wurin kiwon shanu wanda zai magance matsalar kiwon makiyaya da samar da tsarin karatu na zamani da na addini da sauransu.
Duk waɗannan abubuwa da ya yi ba wai ya yi su ba ne a matsayin mai riƙe da muƙamin gwamnati ko tasirin siyasa ba, face sai don ƙudiri da ya ke da shi na kawo sauyi a duniya.
Ayyukansa sun bayyana hoton taimakon al’umma, sannan kuma ba na taɓa ganinsa ko na kira shi a matsayin Oga, shi ɗin shugaba ne.
Congratulations Kashifu kan rayuwarka ta sadaukarwa wacce ke ƙarfafa sauran jama’a. Fatan cigaba da samun ƙarin nasarori. Amin.
-Rotimi Popoola.