Gwamnatin Tarayya ta Tsara N26trn a Matsayin Kasafin Kuɗi na 2024
Najeriya ta tsara naira tiriliyan 26.01 (dala biliyan 33.8) a matsayin kasafin kuɗi na shekarar 2024 da za ta miƙa wa majalisar tarayya domin amincewa kafin ƙarshen watan Disambar bana.
Kasafin ya zarta na bara da gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta yi da dala biliyan 5.7.
Read Also:
An ƙiyasta farashin kowace ganga ɗaya ta man fetur kan dala 73.96, inda ake sa ran ƙasar za ta haƙo ganga miliyan 1.78 a kowace rana, da kuma naira 700 a matsayin darajar naira kan kowace dala ɗaya, a cewar Ministan Kasafin Kuɗi Atiku Bagudu.
Najeriya wadda ita ce mafi girman tattalin arziki a Afirka, na fuskantar matsain tattalin arzikin sakamakon tashin farashin abinci da na kayayyaki, da faɗuwar darajar naira, wadda ta kai N1,000 kan dala ɗaya a kasuwar bayan fage.
Kazalika, akwai ɗumbin bashin da ya kai naira tiriliyan 87.38 (dala biliyan 113.4) d ake bin Najeriyar.
Tun daga watan Mayu, Shugaba Bola Tinubu ya ɗauki matakan tattalin arziki masu wuya, ciki har da zare hannun gwamnati daga kasuwar canjin kuɗi da kuma cire tallafin man fetur.