Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ƙwace kujerar ɗan Majalisar Tarayya, Sanata Abbo

 

Kotun Ɗaukaka Ƙara a Najeriya ta ƙwace nasarar ɗan majalisar tarayya Sanata Ishaku Abbo na jam’iyyar APC mai wakiltar Mazaɓar Adamawa ta Arewa a zaɓen watan Fabarairu da ya gabata.

Ɗan takarar adawa na jam’iyyar PDP, Amos Yohanna, shi ne ya ɗaukaka ƙarar bayan kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta yi watsi da ƙorafinsa, tana mai cewa “ƙorafin bai cancanci a saurare shi ba”.

Sai dai jaridar Daily Trust ta ruwaito kotun ɗaukaka ƙarar da ke zama a Abuja na cewa akwai ƙuri’un da ba halastattu ba cikin waɗanda aka kaɗa wa Mista Abbo bisa la’akari da Dokar Zaɓe ta 2022.

Dalilin haka ne kotun ta soke wasu daga cikin ƙuri’un da aka kaɗa tana mai cewa haramtattu ne, kuma ta ce Mista Yohanna ne ya ci mafi yawan halastattun ƙuri’un da aka kaɗa.

Tawagar alƙalaln uku da ta saurari ƙarar ta kuma umarci hukumar zaɓe ta ƙasa Inec ta bai wa Yohanna na PDP takardar shaidar cin zaɓen.

Wannan hukunci na nufin Mista Abbo ya bar Majalisar Dattawan Najeriya ke nan kasancewar ita ce kotun ƙarshe da ke da hurumin sauraron ƙorafin zaɓen ‘yan majalisa – ma’ana babu sauraron ɗaukaka ƙara.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com