Shugaba Buhari ya Nada Dr. Ifedayo Morayo Adetifa a Matsayin Sabon Darekta Janar na Hukumar NCDC ta Kasa
Dr. Ifedayo Morayo Adetifa zai hau kujerar Darekta-Janar na hukumar NCDC.
Sabon Darektan zai canji Dr. Chikwe Ihekweazu wanda zai tafi kungiyar WHO.
Yemi Osinbajo zai jagoranci kwamitin da zai gyara harkar kiwon lafiya a Jahohi.
Abuja – Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Dr. Ifedayo Morayo Adetifa a matsayin sabon Darekta Janar na hukumar NCDC ta kasa.
Jaridar Daily Trust ta wallafa rahoto cewa fadar shugaban kasa ta tabbatar da wannan nadin mukami a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba, 2021.
NCDC ce hukumar da ta ke yaki da barkewar cututtuka a Najeriya tun bayan da ta samu cin gashin-kai.
Adetifa Morayo Adetifa zai rike NCDC
Kamar yadda shafin LSHTM ya nuna, Dr. Adetifa Morayo Adetifa ya yi digirinsa na farko a jami’ar Ilorin, jahar Kwara a bangaren ilmin likitanci.
Read Also:
Sabon darektan ya kware a harkar ilmin likitancin kananan yara a asibitin koyar da likitoci na jami’ar UNILAG da ke garin Idi-Araba, jahar Legas.
Adetifa ya yi wani digirin a fannin kula da yadda cututtuka suke yadu wa a al’umma. A wannan fanni ya yi digirin PhD a wata jami’ar Amsterdam.
Darektan na NCDC yana aiki ne a makarantar tsabta da ke Landan a kasar Birtaniya, a lokacin da aka ba shi wannan mukami, yana mataimakin Farfesa.
Kafin nan ya yi aiki a kasashen waje, yayi yaki da zazzabin cizon sauro, ya yi bincike a kan tarin tibi.
An ba Osinbajo aiki
Tolu Ogunlesi yace shugaban kasa ya kafa kwamitin da zai gyara sha’ani kiwon lafiya a jihohi da birnin taraya. Yemi Osinbajo ne zai jagoranci kwamitin.
Za a zakulo sauran ‘yan kwamitin ne daga masana da malaman kiwon lafiya. Hadimin shugaban kasar yace za a dauko wakilai daga majalisa da gwamnoni.
Ina Chikwe Ihekweazu?
Sabon darektan, Ifedayo Morayo Adetifa zai karbi Chikwe Ihekweazu wanda labari ya zo cewa ya zama matamakin darekta a hukumar lafiya ta Duniya.
A baya an ji shugaban WHO, Tedros Ghebreyesus ya aiko wa Dr. Chikwe Ihekweazu takarda yana sanar da shi zai zama sabon shugaban bada agajin gaggawa.