Bayan Rasuwar Sarkin Kantagora, Said Umaru Namaska: An Fara Shirin Nada Sabon Sarkin Sudan

 

An fara shirin nada sabon Sarkin Sudan na Masarautar Kontagora a jahar Neja.

Sarkin Sudan ya rasu ne ranar 9 ga Satumba 2021.

Ana zargin daya daga cikin yan kwamitin zaben sarki da rashin gaskiya, yayi murabus.

Niger – Akalla Yarimomi 45 kawo yanzu sun bayyana niyyar na ahwa karagar mulkin Sarkin Sudan na Kontagora.

Wannan ya biyo bayan rasuwar Sarkin Kontagora, Alhaji Said Umaru Namaska, wanda ya rasu bayan shekaru 47 kan mulkin.

Daily Trust ta rawaito cewa kawo yanzu, mutum 21 cikin wadanda suka dauki takardar takara sun kammala cikawa kuma sun dawo da shi.

Shugaban kwamitin zaben Sarki, Alhaji Shehu Galadima, ya bayyanawa manema labarai cewa mambobin kwamitinsa zasu tabbatar da cewa an yi zaben gaskiya da lumana.

Yace:

“Muna addu’a, kuma zamu tabbatar da cewa an kafa tarihi da wannan zabe. Mun lashi takobin yin adalci bisa ka’idojin zaben domin tabbatar ba’ayi son kai ba.”

Wani mamban dattawan masarautar, Manjo Janar Suleiman Saidu (mai ritaya) yace babu wanda zai samu fifiko wajen kwamitin zaben.

Yace:

“Kujerar Sarkin Sudan na Kontagora na daga cikin manyan kujerun sarauta a Arewacin Najeriya; saboda haka, ya kamata mu bi a hankali.”

“Masu zaben Sarki subi ka’ida wajen zabe kamar yadda aka bukacesu.”

Ana zargin daya daga cikin mambobin kwamitin zabe

Daya daga cikin mambobin kwamitin wanda shine Sakataren kwamitin, Ahmed Tijjani, ya yi murabus daga kujerar.

Wata majiya ta bayyana cewa ya yi murabus ne sakamakon kararraki da wasu yan takara suka shigar kansa a ma’aikatar kananan hukumomi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here