NAFDAC ta Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Siyan Daskararrun Kaji

 

Hukumar NAFDAC ta bayyana gargadi ga mutanen da ke sayen kajin kasar waje da ke zuwa a daskare.

Hukumar ta ce, akwai illar da ke tattare da sinadarin da ake sanya wa a cikin kajin domin kada su baci.

Hukumar ta kuma ce, sayen kajin waje zai durkusar da tattalin arzikin ‘yan kasuwan cikin gida.

Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) a jiya ta gargadi ‘yan Najeriya da su guji cin daskararrun kayayyakin kaji da sauran kayayyakin abinci da aka adana da sinadarin Formalin.

Formalin wani sinadari ne mai guba wanda aka fi amfani da shi don adana gawa domin kada jikin mutum ya lalace, The Nation ta rawaito.

Kakakin NAFDAC, Dakta Abubakar Jimoh, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja cewa wasu mutane suna amfani da sinadarin Formalin don adana kaji da sauran nau’ikan nama.

Formalin yana da karfin adana irin wadannan samfuran abinci na tsawon makonni kafin su isa ga masu amfani dasu.

A cewar Jimoh

“NAFDAC tana fadakar da ‘yan Najeriya kan wannan abu. Akwai isassun nau’ikan kaji a cikin kasar fiye da yin amfani da daskararrun kaji da aka shigo da su, baya ga haramcin Gwamnatin Tarayya.”

Kakakin NAFDAC ya kuma ja hankalin masu amfani da daskararrun kajin da ake shigo dasu da su duba yanayin tattalin arzikin wajen sayen kajin cikin gida.

Ya lura cewa idan aka ci gaba da sayen kayan waje, manoman kaji da ‘yan kasuwa na gida ba za su girma yadda ake so ba, saboda kudin da ake kashewa kan kayayyakin fasa-kwaurin zai tafi ne kawai ga wasu mutane a waje.

Jimoh ya kara da cewa, kula da kayayyakin da aka shigo da su daga kasashen waje ko kuma na fasa kwaurin za su ci gaba da yin illa ga taskar kudaden waje na Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here