Sojojin Najeriya Sun Hada Kai da Kasar Rasha ta Fannin Sojoji da Fasaha

 

Gwamnatin Najeriya ta sake rattaba hannu da kasar Rasha ta fannin sojoji da fasaha.

Wannan na zuwa ne bayan karewar wa’adin yarjejeniyar ta shekaru da suka gabata.

Legit ta tattaro manufar wannan yarjejeniya da gwamnatin Najeriya ta kullo da Rasha.

Russia – Gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa ta fasaha da sojoji tare da tarayyar Rasha.

Wata sanarwa da rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar a ranar Laraba, 25 ga watan Agusta na nuna cewa ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (Rtd), wanda ke kan ziyarar aiki a kasar Rasha, ya sanya hannu a madadin Najeriya.

Legit.ng ta tattaro cewa daraktan ma’aikatan tarayya na hadin gwiwar sojoji da fasaha, Dmitry Shugaev, ya rattaba hannu a madadin tarayyar Rasha.

Jawabin sanya hannun wanda ya gudana a ranar Litinin, ya samu shaidar jakadan Najeriya a Rasha, Farfesa Abdullahi Y. Shehu, Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Vice Admiral Auwal Zubairu Gambo, da sauran kusoshin tsaro.

Sauran wadanda suka halarci taron sune wakilan Sojojin Najeriya da Sojojin Sama na Najeriya, wasu manyan hafsoshin sojoji, da jami’an ma’aikatar tsaron Najeriya.

An tattaro cewa sabuwar yarjejeniyar ta kawo karshen yarjejeniyar farko da kasashen biyu suka kulla wadda aka kulla a ranar 6 ga Maris, 2001.

A cikin takaitaccen bayani bayan rattaba hannu, Ambasada Shehu ya nuna godiya ga mahukuntan Rasha kuma ya nanata cewa Najeriya ba ta neman komai a hadin gwiwar dace dacewa da fa’idodin juna.

Manufar yarjejeniyar

Legit.ng ta tattaro cewa yarjejeniya kan hadin gwiwar soji da fasaha tsakanin kasashen biyu yana ba da tsarin doka na samar da kayan aikin sojoji, ba da sabis bayan sayen makamai, horar da ma’aikata a cibiyoyin ilimi daban-daban da canja wurin fasaha, da sauran su.

Rattaba hannu kan yarjejeniyar wani babban ci gaba ne a alakar da ke tsakanin Najeriya da Rasha.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here