Sabon Hari: An Kama Mutane 10 da Ake Zargi a Jahar Plateau

 

An kama mutane 10 da ake zargin suna da hannu a sabon harin da aka kai kauyen Yelwa Zangam da ke Jos ta arewa, jahar Filato.

Gwamnan jahar, Simon Lalong, ya kwatanta lamarin da zalunci inda ya yi kiran taro na gaggawa dake da alaka da tsaron yankin.

Gwamnan ya bukaci jami’an tsaro da su yi gaggawar ganin sun bi diddigi wurin gano wadanda suka yi kisar da masu daukar nauyi.

Jos, Plateau – An kama mutane 10 da suke da alaka da kai sabon hari kauyen Yelwa Zangam na Jos ta arewa da ke jahar Filato, Daily Trust ta rawaito hakan.

Gwamna Simon Lalong ya kwatanta harin a matsayin rashin imani, sannan ya shirya taro na gaggawa don tattaunawa da kuma neman hanyar kawo garanbawul ga kashe-kashen da aka maimaita a jaharsa.

A wata takarda wacce darektan watsa labarai ya saki, Makut Mechan, ya ce gwamnan ya umarci jami’an tsaro su binciko duk wadanda suke da hannu a lamarin da masu daukar nauyinsu don a hukunta su.

Lalong ya fusata a kan lamarin wanda rahotanni daga jami’an tsaro sun nuna cewa shirya su aka yi tsaf sakamakon yadda aka lalata gadar da take kai mutane zuwa kauyen don a hana jami’an tsaro zuwa wurin da aka kai harin,” kamar yadda takardar ta shaida.

Gwamna Lalong ya kara da jan kunnen ‘yan ta’addan, inda ya ce za a bi bayan su, a kama su sannan komin daren dadewa, mulkinsa ba zai taba barin ta’addanci ya ci gaba ba.

Hakazalika, zai yi iyakar kokarin ganin ya dawo da zaman lafiya a jahar, kamar yadda yace.

Sai dai Kakakin hukumar ‘yan sanda, ASP Ubah Gabriel, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Daily Trust ta rawaito yadda wani mazaunin yankin, Yakubu Bagudu yake cewa an kashe fiye da mutane 30 a tsakiyan daren Talata sakamakon farmakin.

Bagudu ya kara bayyana yadda aka kona gawawwakin wasu daga cikin wadanda aka kashe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here