Canja Sheka: Femi Fani Kayode ya Caccaki Mataimakin Gwamna Matawalle, Mahdi Gusau

 

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya caccaki mataimakin gwamnan jahar Zamfara, Mahdi Gusau.

Hakan ya biyo bayan kin canja shekar da yayi daga jam’iyyar PDP zuwa APC bayan gwamnansa, Bello Matawalle, ya canza.

Tsohon ministan ya yi wannan caccakar ne ta wata wallafa da yayi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta ranar Talata.

FCT, Abuja – Tsohon ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode (Sadaukin Shinkafi) ya yi wa Mataimakin Gwamnan jahar Zamfara, Mahdi Gusau, wankin babban bargo a kan kin komawa jam’iyyar APC.

A wata wallafa da Tsohon ministan yayi ta shafinsa na Twitter, wanda shi din jigo ne na jam’iyyar PDP, ya ce Mahdi bai nuna da’a ba ga gwamnansa, Bello Matawalle, wanda ya canja sheka daga PDP zuwa APC, premium times ta rawaito.

Gwamnan jahar Zamfara tare da ‘yan majalisar jahar da sauran kwamishinonin jahar sun koma jam’iyyar APC a watan Yuli, bayan watanni kadan da gwamna Ben Ayade na jahar Cross River da David Umahi na jahar Ebonyi suka koma jam’iyya mai mulkin.

Idan gwamna ya koma wata jam’iyya, mai zai hana mataimakinsa koma wa? Gwamna Bello Matawalle bai zabi kowa ya kasance mataimakinsa ba sai kai, amma mai zai sa ka yi masa rashin da’a kuma ka ci amanarsa?.

Premium Times ta rawaito cewa, tsohon ministan yana matukar caccakar APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari sosai kuma ya dade yana musanta batun zai sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here