Shugaba Buhari ya Magantu Kan Harin ‘Yan Bindiga a NDA

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi martani kan harin da ‘yan bindiga suka kai NDA.

Ya ce, wannan ya kamata ya zama izina, ya kuma zama sanadin da zai sa a kara kaimi wajen yakar ‘yan bindiga.

Ya kuma ce, ‘yan ta’adda na ci gaba da fuskantar fushin jami’an sojojin Najeriya, don haka dole a dage.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce harin baya-bayan nan da aka kai Cibiyar Kwalejin Tsaro ta Najeriya (NDA) a Kaduna zai taimaka wajen kara azama, kaimi da sa karfin sojoji wajen kawo karshen tashin hankali a kasar.

Shugaban na Najeriya ya bayyana cewa:

“Wannan mummunan aikin zai hanzarta kawar da munanan abubuwan da ke faruwa, wanda membobin rundunar sojojin suka kuduri aniyar aiwatarwa cikin kankanin lokaci.”

A cikin wata sanarwa da daya daga cikin masu taimaka masa a bangaren yada labarai, Femi Adesina, ya ce, shugaban ya lura cewa mugun nufin da masu aikata laifuka ke yi don rage martabar sojojin kasar a idon duniya ya gaza.

Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da sojoji ke ragargazar masu tayar da kayar baya, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da sauran ire-iren masu aikata miyagun laifuka, musamman a arewa maso gabas.

Ya kamata ‘yan Najeriya su ke yabawa sojojin Najeriya

A bangare guda na sanarwar, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, duba da namijin aikin sojojin Najeriya ke yi ya kamata ‘yan Najeriya suke yaba musu, hakanan ya godewa ‘yan Najeriyan da ke yabawa sojoji.

Adesina a cikin sanarwar yana cewa:

“Shugaban ya gode wa dukkan ‘yan Najeriya da ke darajawa da yaba kokarin sojojinmu, kuma yana kira ga wadanda ke sa siyasar kiyayya a lamarin tare da munanan ayyuka da su guji hakan, lura cewa maimakon adawa, wannan lokaci ne ga duk masu kishin kasa da mutanen da ke da niyyar tallafawa su karfafawa dakaru a fagen daga.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here