Najeriya na da Isassun Likitoci Amma Sun Gudu Abuja, Legas da Fatakwal – Ngige
Ministan Kwadago ya ce Likitocin Najeriya sun tare a birane shiyasa ake ganin babu Likitoci.
Ngige ya yi tsokaci ne kan yadda Likitoci ke guduwa daga Najeriya.
Wata daya kenan da Likitocin Najeriya suka shiga yajin aiki.
Abuja – Ministan Kwadagon Najeriya, Chris Ngige, yace Najeriya na da isassun Likitoci amma yawancinsu sun gudu aiki birnin tarayya Abuja, Legas da garin Fatakwal.
Ngige ya bayyana hakan ne a taron kwamishanonin lafiyan jahohin Najeriya a ranar Juma’a, 3 ga Satumba, 2021.
Kamfanin dillancin Labarai NAN ta ruwaito cewa an shirya taron ne don tattauna yadda za;a inganta kiwon lafiya a Najeriya.
Read Also:
Ngige yace Najeriya Najeriya ba zata iya cika sharadin majalisar dinkin duniya ba na yawan Likitocin da ya kamata ace kasa na da shi.
Yace:
“Mu ba kasar majalisar dinkin duniya bane, mu kasa ce mai cigaba. Saboda haka zamuyi amfani da abin da muke dashi.”
“Likitoci nawa muke da shi a karkara tun da kowa ya gudu birni. Kusan kowa ya dawo Abuja, Legas da Fatakwal da zama. Kuma muna da asibitoci 10,000 kuma babu Likitoci.”
Duk laifin gwamnonin Najeriya ne
A taron, Kwamishanan Lafiya jahar Legas, Abayomi Akin, ya yi kira ga gwamnonin Najeriya su inganta lamarin lafiya ga Likitoci a jahohinsu.
Abayomi yace akwai Likitocin Najeriya sama da 20,000 dake aiki a kasar waje yanzu.
Yace:
“Shiyasa nike kira ga gwamnoni sun inganta abubuwa don Likitoci. Yanzu ba maganar guduwar Likitoci kasashen waje ya kamata mu rika magana kai ba, kamata yayi muyi magana kan dawo da su.”