Gwamnatin Ganduje ta ki Biyana Kudin Fansho – Kwankwaso

 

Kwankwaso ya yi korafin yadda gwamna Ganduje ke take masa hakkinsa.

Tsohon gwamnan yace ba’a biyansa kudin fanshon wata-wata da ya kamata.

Kwankwaso ya hadu da Ganduje a filin jirgin sama a Abuja makon da ya gabata.

Tsohon Gwamnan Jahar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa gwamnatin jahar Kano karkashin Gwamna Abdullahi Ganduje na take masa hakkinsa.

Kwankwaso ya yi korafin cewa shekara shida kenan Ganduje ya ki biyansa kudin fansho, ya ki gina masa gida kamar dokar jahar ta tanada.

Hakazalika gwamna Ganduje bai gina masa ofishin da doka ta bukaceshi ba.

Kwankwaso ya ce an yi hakan ne da gangan saboda ya koma jam’iyyar hamayya.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da BBC Hausa.

A cewarsa:

“Da ace ina tare da su, da sun biya ni kudaden fansho na a kowanne wata. Na yarda hakan na faruwa ne saboda ina bangaren adawa. Saboda haka su je su rike.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here