Najeriya za ta Ci gaba da Kasancewa ƙasa daya – Shugaba Buhari

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabannin siyasa akan su mayar da hankalinsu don tabbatar da babbar manufar raya buƙatun kasa, yana cewa “mu ƴan Najeriya ne, kuma da ikon Allah za mu cigaba da kasancewa ƴan Najeriya, sannan Najeriya za ta ci gaba da kasancewa ƙasa daya.”

Shugaba Buhari wanda ya fadi hakan a jiya Talata yayin ƙarɓar baƙuncin tsohon shugaban tsohuwar jam’iyyar CPC a fadarsa, ya ce ya lura sha’awa da ƙoƙarin bunƙasa rayuwar ƴan Najeriya bai gushe a zuƙatan mutane ba, yana mai kira da su sake jajircewa.

Shugaban ya ƙara da cewa bai kamata a maimaita son kan da ya yi dalilin asarar rayuka kusan miliyan ɗaya daga shekarar 1967 zuwa 1970 ba.

Buhari yana wannan magana ne da alaƙantata da yaƙin basasar ƙasar na wancan lokaci.

Ya ce ya kamata kuma a yi duk abun da ya kamata wajen ganin haka bai sake faruwa ba, in da ya ƙara da cewa an samar da CPC ne akan gimshiƙin kishin ƙasa da amana dangane da haɗin kan Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here