Najeriya: Labaran ƙarya da aka Yaɗa kan Zanga-Zangar EndSars

A farkon watan nan ne dai aka fara wata zanga-zanga a Najeriya inda matasan ƙasar suka yi kira da a rushe rundunar da ke yaƙi da fashi da makami ta SARS.

Batun wannan zanga-zangar ya bazu a duniya musamman a kafofin sada zumunta inda aka wallafa abubuwa da dama, amma ba duka ba ne gaskiya.

Mun tattaro muku wasu daga cikin labaran ƙarya da aka baza kan wannan lamari.

Matar da ke zanga-zanga wadda aka yi ƙaryar cewa’yan sanda sun kashe mata ‘yan uwa
Akwai wani hoto mai ban tausayi na wata mata da ake kira Blessing Ugochukwu inda aka ga tana kuka riƙe da tutar Najeriya a naɗe inda take zaune kan wani butunbutumi, an dai yaɗa wannan hoton matuƙa a shafin Twitter.

Hoton da gaske ne, kuma ta shiga zanga-zangar a kudu maso gabashin Najeriya. Sai dai a daidai lokacin da ake yaɗa hoton, sai mutane suka rinƙa ƙarin bayani na ƙarya kan hoton.

“Ba ɗan uwa ɗaya ba, uku a ranar ɗaya, aka kashe aka jefa su cikin rijiya,” wannan na daga cikin irin martanin da mutane suka mayar kan hoton inda ake iƙirarin ta rasa ‘yan uwanta a hannun ‘yan sanda.

Ko da BBC ta tuntuɓi wani da ya yi magana da yawun Ms Ugochukwu wanda ake kira Gideon Obianime, ya bayyana mana cewa wannan batu ba gaskiya ba ne.

Ya bayyana cewa ita kanta Ms Ugochukwu ɗin ‘yan sandan SARS ɗin sun taɓa tsare ta na lokaci kaɗan a 2018, amma duk da cewa tana da ‘yan uwa maza, babu wanda SARS suka taɓa kashewa.

“Ina tunanin mutane sun fara faɗin ra’ayin kansu ne kan wannan hoto. Ana ta caccakarta kan wannan hoton, kamar yadda Misa Obianime ya shaida wa BBC
Ɗaukar tutar Najeriya ba zai kare ku daga sojojin ƙasar ba

Wannan iƙirarin da ake yi ya karaɗe shafukan sada zumunta inda ake cewa soja ba zai iya harbin wanda ke riƙe da tutar ƙasar ba.

An yaɗa hakan matuƙa a Twitter da Facebook da Instagram inda wasu ke cewa akwai wata doka ta soji da ta yi umarni da hakan duk da ba rubutacciya ba ce.

Ana zargin wannan iƙirarin ya samo asali ne kan wata tattaunawa da wasu suka yi da aka ɗauki hotonta inda wani ke cewa mahaifinsu ne ya bayyana musu hakan, wanda kuma tsohon soja ne.

Wasu sun ta mayar da martani inda suke cewa: “Ina tunanin wannan dokar soja ce…Ku yi ta yaɗa hakan yadda masu zanga-zanga za su sani.”

Sai dai babu wata hujja kan wannan lamarin, kuma akwai shafuka da dama da suka wallafa wannan batu da tuni suka goge bayan wasu sun fito sun fara cewa wannan labarin na ƙarya ne.

Onyekachi Umah, wanda lauya ne a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa akwai wasu dokoki kan girmama tutar ƙasa, amma ya ƙara da cewa “Kawai don mutum na riƙe da tuta ba yana nufin cewa sojoji ba za su iya yin wani abu ba.”

Sai dai wani ɗan jarida a Najeriya ya ce ya tambayi wani babban tsohon soja kan ko lamarin gaskiya ne inda ya shaida masa cewa hakan ba gaskiya bane

A’a babu wani babban jami’in Najeriya da ya kira wannan zanga-zangar wasan yara

Bayan kwanaki da aka fara gudanar da wannan zanga-zanga, an wallafa wani bidiyo a kafafen sada zumunta inda yake nuna ɗaya daga cikin masu ba Shugaba Buhari shawara, Femi Adesina, inda yake kiran masu zanga-zangar “wasan yara”.

Wasu da dama sun fassara wannan kalaman na Mista Adesina a matsayin Shugaba Buhari na watsi da wannan zanga-zangar.

Kuma bidiyon na ɗauke da saƙo: “Idan ba ka ji haushi sosai ba, ina fatan wannan bidiyon zai taimake ka.”

Sai dai wannan bidiyon tsoho ne kuma an sauya shi kan turbarsa.

Bidiyon na da alaƙa ne da wasu zanga-zanga da aka gudanar a baya watanni biyu da suka gabata – bai da alaƙa kwata-kwata da SARS.

A lokacin da aka yi wa Mista Adesina bidiyon, yana hira da wata kafar watsa labarai ta ƙasar ne inda yake magana kan zanga-zangar, sai dai bidiyon da aka wallafa a Twitter an yi masa kwaskwarima inda aka yanke farkon bayanin nasa wanda ya kamata ya fahimtar da mutane kan ainahin batun da ake magana a kai.

Ya yi hirar ne a gidan Talabijin na Channels, kuma gidan talabijin ɗin ya yi ƙarin haske kan labarin ƙaryar da aka rinƙa yaɗawa na bidiyon.

Shi kan shi Mista Adesina ya fitar da sanarwa inda ya gode wa gidan talabijin ɗin da fitowa ya yi bayani, inda kuma ya ce wannan labarin ƙaryar ya ja wayarsa ta cika da saƙonni na zagi da cin mutunci
Malaman cocin Katolika da kuma masu zanga-zangar SARS
Wani saƙon Twitter da aka yaɗa fiye da sau dubu ya yi iƙirari na ƙarya kan cewa wasu malam ɗarikar katolika sun fito wani tattaki domin goyon bayan masu zanga-zangar ENDSARS.

Saƙon na Twitter ya nuna wasu malaman na katolika cikin taron jama’a masu tattaki, akasarinsu suna sanye da baƙaƙen kaya, inda wasu kuma ke riƙe da alluna.

Sai dai wannan hoton tsohon hoto ne, domin wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa malaman sun gudanar da wannan zanga-zangar ne a watan Maris a Abuja inda suka fito domin nuna rashin jin daɗinsu kan kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane da ake yi a ƙasar.

Sai dai a wani ɓangaren, ƙungiyar malaman na katolika ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa inda take goyon bayan wannan zanga-zangar, amma ‘ya’yanta ba su fitokan tituna su nyi irin wannan zanga-zangar ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here