Najeriya za ta Hada-Kai da Masar Domin a Samu Wutar Lantarki – Abubakar Aliyu

 

Ministan harkokin lantarki, Abubakar Aliyu ya zauna da Jakadan kasar Masar.

Abubakar Aliyu yace Najeriya za ta hada-kai da Masar domin a samu lantarki.

Ganawar ta biyo bayan zaman da Buhari ya yi da Abdul Fattah al-Sisi a Abuja.

Abuja – Ministan harkokin lantarki, Abubakar Aliyu, yace gwamnatin tarayya zata duba yadda za ta iya hada kai da Masar domin a inganta samun wuta.

Daily Trust tace Ministan ya bayyana wannan ne yayin da ya gana da Jakadan Masar a Najeriya, Ilhab Awab a ranar Talata, 14 ga watan Satumba, 2021.

“Na san da zaman da kuka yi da wanda na gada, wanda hakan ya kai ga rubuta takadar cin ma yarjejeniya da aka aiko mana daga ma’aikatar harkokin kasar waje.”

“Har zuwa ga gayyatar da gwamnatinku ta aiko mana zuwa Masar.”

“Ziyarar da ka kawo yanzu ya bada dama a karfafa wannan alaka. Ka yi bayanin yadda kuka yi nasara wajen shawo kan matsalar wuta a kasar Masar.”

“A matsayinka na Jakada a Najeriya, ka dauki tsawon lokaci a nan. Ka san yadda muke fama da wannan matsala a kasar nan.”

Za a dage kan matsalar wuta – Minista Jaridar a rahoto Abubakar Aliyu yana cewa gwamnatin Najeriya za ta farfado da zumuncin da ke tsakanin kasashen domin ayi maganin matsalar rashin wuta.

Ministan yace za a tura tawaga daga ma’aikatar Najeriya da za ta samu lokaci ta ziyarci kasar Masar, da nufin a dauki darasi a kan yunkurin da aka yi a can.

A cewar Ministan, shugaba Muhammadu Buhari da gaske yake yi wajen gyara matsalar wutar lantarki don haka ne ya gana da Abdul Fattah al-Sisi kwanaki.

A lokacin da shugaban Masar, Abdul Fattah al-Sisi ya ziyarci Najeriya a shekarar 2019. Awab yace sun yi maganar yadda za a iya inganta rabon wutar lantarkin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here