Najeriya: Muna Kan Aikin Samar da Filayen Jiragen Sama Guda Goma
Gwamnatin Najeriya ta bada sanarwar cewa yanzu haka tana kan aikin samar da filayen sauka da tashin jiragen sama guda goma a wasu jihohin kasar don bunƙasa tattalin arzikinta.
Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Hadi Sirika ne ya bayyana hakan yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattijan ƙasar mai kula da harkokin sufurin jiragen sama a ranar Talata don kare kasafin kudin ma’aikatarsa na shekarar 2021.
Read Also:
Kwamitin majalisar ya bayyana damuwa dangane da yadda wasu filayen jiragen sama da ke ƙasar suka lalace.
Hadi Sirika ya ce a yanzu gwamnati na kallon bangaren sufurin jiragen sama a matsayin wata hanya ta bunƙasa tattalin arzikinta, shi ya sa ma ta ɗauki gaɓarar gina filayen sauka da tashin jiragen sama a jihar Anambra, da Benue, da Ekiti, da Nasarawa da Ebonyi.
Sannan ya ce tuni gwamnatin tarayya ta karɓi ragamar filayen sauka da tashin jiragen sama na Dutse, da Osubi, da Kebbi daga gwamnatocin jihohin, sannan ita ma gwamnatin jihar Gombe ta rubuta wasikar neman gwamnatin tarayyar ta karbi ragamar filin sauka da tashin jiragen samanta