Adadin Megawatt na Wutar Lantarki da Najeriya ta rage bai wa Nijar
Najeriya ta rage wutar lantarkin da ta ke sayarwa Jamhuriyar Nijar da ke ƙarƙashin mulkin soja daga Megawatt 80 zuwa megawatt 46.
Hakan na nun cewa an raguwar wutar lantarki da kashi 42 cikin ɗari ga ƙasar. Ministar makamashi ta Nijar, Haoua Amadou, ta ce matakin ya sa wutar lantarkin ƙasar ya ragu da tsakanin kashi 30 zuwa 50 cikin 100, kuma ya tilasta wa kamfanin samar da wutar lantarki mallakar gwamnati Nigelec aiwatar da shirin rage wutar lantarki da ake rarrabawa zuwa sassan kasar wanda ka iya ɗaukar kwanaki da dama, musamman a birnin Yamai.
Read Also:
Najeriya ta dakatar da wutar lantarkin da take fitarwa zuwa makwabciyarta a wani ɓangare na takunkumin da aka ƙaƙabawa gwamnatin mulkin soji da ta hambarar da shugaban farar hula Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.
”Tuni dai Najeriya ta dawo samar da wutar lantarki amma tana samar da megawatt 46 maimakon megawatt 80 da aka saba,” in ji Amadou
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ita kanta Najeriyar ke fama da ƙarancin wutar lantarki saboda karancin iskar gas da kuma ƙarancin zuba jari a ɓangaren makamshin ƙasar.
A halin yanzu ƙasar na samar da kimanin 5000mw, wanda da kyar ya ke isar al’ummarta,
Masana sun ce Najeriya na buƙatar aƙalla megawatt 30,000 kafin a samu wadatar wutar lantaki a ƙasar.