Kungiyar NANS na Koka Kan Rashin Tsaro da Dalibai ke Fuskanta
Kungiyar dalibai a Najeriya ta bayyana bukatar ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.
Wannan na fito wa ne daga bakin shugaban NANS a ranar Lahadi 8 ga watan Agustan 2021.
Ya yi kira da gwamnati ta inganta lamarin tsaro a dukkan makarantun dake fadin Najeriya.
Ekiti – Kungiyar Daliban Najeriya ta kasa (NANS) ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya ayyana barayin da ke sace dalibai a yankin arewacin kasar a matsayin ‘yan ta’adda.
Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban NANS na kasa, Sunday Asefon, ya yi wannan kiran ne a madadin kungiyar a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, a Ado-Ekiti, jahar Ekiti.
Legit.ng ta tattaro cewa Asefon ya ce duk wanda ke da halin yin garkuwa da kashe dalibai to a bayyana shi a matsayin dan ta’adda kawai.
Ya yi Allah wadai da rufe wasu makarantu a wasu sassan arewacin kasar saboda karuwar satar dalibai, Nigerian Tribune ta kuma bayyana.
Read Also:
NANS ta gana da Sheikh Gumi A halin da ake ciki,
Asefon ya kuma bayyana cewa NANS ta gana da shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmed Gumi, kan halin da ake ciki na sace dalibai.
Ya ce an bukaci malamin addinin Islama da ya fada wa ‘yan bindigar da su guji makarantun gwamnati da ‘ya’yan talakawa ke karatu.
Sheikh Gumi wanda ke iya kokarinsa don dakatar da ‘yan bindiga daga kara aikata munanan ayyuka yakan bayyana bukatar gwamnati ta tattauna da ‘yan bindigan.
Ya kamata gwamnati ta inganta tsaro Asefon ya kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta karfafa tsaro a makarantu, lura da cewa ya kamata dalibai su iya zuwa makaranta ba tare da fargabar rashin tsaro ba.
A cewarsa:
“Ya kamata gwamnati ta karfafa tsaro a makarantu.
Imanin mu ne cewa yakamata ɗalibai su tafi makarantu tare da tabbacin za su sami tsaro.
“Ina kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana wadannan barayin da ke sace dalibai a arewa maso yamma da arewa ta tsakiya a matsayin ‘yan ta’adda.”