ASUU: NANS ta yi Martani Kan Komawa Yajin Aiki

 

Kungiyar daliban Najeriya ta tabbatar da cewa za ta fada gagarumar zanga-zanga idan ASUU ta koma yajin aiki.

Kungaiyar ta ce abun kunya ne da takaici yadda kungiyar tace ta janye yajin aikinta amma da sharadi.

Matukar kuwa kungiyar ta koma yajin aiki, daliban Najeriya za su fita kwan su da kwarkwata domin zanga-zanga.

Kungiyar daliban Najeriya ta ce mambobinta za su shiga gagarumar zanga-zanga idan har kungiyar malamai masu koyarwa a jami’o’i suka sake fadawa yajin aikin.

Shugaban NANS, Sunday Asefon, ya sanar da hakan a wata tattaunawa da jaridar The Punch a ranar Alhamis.

Ya ce abun kunya ne da takaici yadda ASUU take sake barazanar sabon yajin aiki bayan bata wa daliban Najeriya watanni tara a banza.

Asefon ya ce, “Wannan abun kunya ne a garemu da ASUU tace ta janye yajin aiki amma da sharadi.Idan suka koma aiki da sharadi, mu ma za mu tsaya da shirin mu na fara zanga-zanga.

“Amma idan suka koma yajin aiki, za mu hau tituna tunda yaren da kadai suke ganewa kenan, shi za mu yi musu.”

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi, a ranar Laraba a Abuja ya sanar da janye yajin aikin da aka kwashe watannin tara ana yi amma da sharadi.

Ogunyemi wanda yace an janye yajin aikin a ranar Alhamis, 24 ga watan Disambano 2020, ya tabbatar da cewa kungiyar za ta sake komawa yajin aikin matuukar gwamnati ta kasa cika alkawarinta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here