Sheikh Ahmed Lemu: Abubuwa Game da Marigayin

 

Allah ya yiwa shahararren malamin nan na addinin Musulunci da ke Najeriya, Sheikh Ahmed Lemu rasuwa.

Shehin malamin ya rasu ne a safiyar yau Alhamis, 24 ga watan Disamba a garin Minna, babbar birnin jihar Niger.

Ya rasu yana da shekara 91 a duniya. Daya daga cikin yayan marigayin, Maryam Lemu, ta tabbatar da mutuwar mahaifinsu a wata sanarwa a Facebook, ta ce idan anjima kadan za a soma shirye-shiryen binne shi.

Ga jerin abubuwa da ya kamata ka sani game da shahararren malamin addinin:

1. An haifi Dr. Shaikh Ahmad Lemu a garin Lemu, jihar Neja ranar 21/12/1929.

2. Ya yi karatunsa na Qur’ani a 1932, firamare 1 1939, sakandare a 1948, kwalejin ilmin shair’a dake Lemu a 1950, sannan NCE Arabic a 1952.

3. A 1954, ya tafi jami’ar Landan a kasar Birtaniya inda yayi karatun tarihi, Hausa, da yaren Farisa a 1961, sannan ya samu digiri kan karatun nahiyar Afrika a 1964.

4. Ya karantar da dalibai na sama da shekaru 50 a rayuwarsa.

5. Duk da karantarwan da yake yi, ya kasance Alkali inda ya zama Alkalin kotun shari’a na farko a kotun daukaka karan Sokoto da Neja (1976 – 1977) sannan ya zama babban Alkalin jihar Neja (1976 – 1991).

6. Dr. Shaikh Ahmed Lemu ya auri baturiya, Aisha Lemu, kuma suna da yara da suka shahara wajen da’awar addinin Musulunci. Daga cikinsu akwai Sheikh Nurudeen Lemu da Malama Maryam Lemu.

7. Marigayin ya kasance mai da’awar addinin Musulunci inda ya kafa cibiyar ‘Islamic Education Trust’ (IET) mai hedkwata a Minna, jihar Neja.

8. Lemu ya samu kyaututtuka da lambar yabo da dama a rayuwarsa. Daga ciki ya samu lambar yabon jarumin kasa daga wajen shugaban kasan mulkin Soja, Abdus Salam Abubakar a 1999 da kuma lokacin shugaba Olusegun Obasanjo a 2001.

Hakazalika ya samu doktora na karamci daga jami’ar Danfodiyo a 1996, jami’ar Osun a 2011, da jami’ar Al-Hilal dake Masar a 2013.

(An samu bayanai a shafin lambar yabon King Faisal)

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here