Kungiyar NANS ta yi Martani Kan Yajin Aiki
Kungiyar NANS ta ce dalibai sun gaji da yajin-aikin da Malaman Jami’a su ke yi.
Shugaban kungiyar Daliban yace za su zauna da shugabannin ASUU da gwamnati.
Sunday Asefon ya ce za su rufe Jami’o’in kudi da ke Najeriya idan abu ya ci tura.
Sunday Asefon, sabon shugaban kungiyar daliban Najeriya, ya sha alwashin rufe jami’o’in kudi na ‘yan kasuwa idan aka cigaba da yajin-aiki.
Jaridar Punch ta rahoto Sunday Asefon yana bayani, yace muddin aka zarce da yajin-aikin da ake yi a jami’o’in kasar, lallai za su dauki mataki.
Read Also:
Shugaban daliban ya bayyana haka lokacin da jaridar ta tattauna da shi a shirin The Roundtable.
A cewarsa, NANS za ta zauna da wakilan gwamnatin tarayya da bangaren shugabannin kungiyar malaman jami’a na ASUU domin a samu mafita.
Kwamred Asefon ya bayyana cewa muddin aka gaza samun mafita bayan NANS ta zauna da gwamnatin tarayya da ASUU, za su rufe makarantu.
“A tarihin ASUU, wannan shi ne yajin-aikin da ya fi kowane tsawo, an yi watanni tara yanzu. Gwamnatina ba ta jin dadin wannan.” Inji Asefon.
“Zamu yi zama da wakilan gwamnatin tarayya da na kungiyar ASUU domin ganin yadda za a samu maslaha, saboda dalibai su koma makaranta.” Afeson ya ke cewa:
“Dole a samu mafita mai wanzu wa, ASUU ta daina yajin-aiki, gwamnati ta kuma saurari ASUU. Su ji tausayin daliban da ke gida.”