Rashin Biyan Albashi: Kungiyar NARD ta yi Allah-Wadai da Gwamnatin Jahar Abia

 

Kungiyar NARD tace akwai Likitocinta da sun yi wata da watanni babu albashi.

A jahar Abia, NARD ta na zargin gwamna da kin biyan albashin watanni har 19.

Likitocin da ke yajin-aikin sun ce alawus din hadarin da ake ba su, ya yi kadan.

Abia – Kungiyar NARD ta likitocin da ke neman kware wa a kan aiki ta yi Allah-wadai da gwamnatin da Okezie Ikpeazu yake jagoranta a Abia.

Ikpeazu ya saba alkawari

Kamar yadda muka samu rahoto daga gidan talabijin Channels TV a ranar Alhamis, gwamnatin Abia ta shafe watanni 19 ba ta biya likitoci albashi ba.

A wani jawabi da NARD ta fitar a ranar 26 ga watan Agusta, 2021, bayan zaman da majalisar kolin NEC ta yi a garin Benin, ta yi tir da halin da ake ciki.

“Majalisar NEC ta ji takaici, amma ba ta yi mamaki da gwamnan jahar Abia yaki biyan kudin watanni 19 da ‘yan kungiyarmu ke bin shi bashi ba.”

“Gwamnan (na Abia) ya yi alkawarin zai biya wadannan kudi ne tun kwanaki 23 da suka wuce.”

Akwai wasu jahohin da likitoci ke wahala?

Haka zalika, kungiyar ta NARD tace likitocinta suna bin gwamnonin Imo, Ekiti da Ondo bashin albashinsu na tsawon watanni goma, shida da kuma hudu.

Takardar bayan taron da NARD ta fitar ya kuma bayyana cewa akwai likitoci 114 da aka yi wata daya zuwa watanni hudu ba tare da sun ci daga guminsu ba.

A game da alawus din da ake ware wa ma’aikatan lafiya saboda yiwuwar aukuwar wani hadari a a asibitoci, NARD tace N5, 000 a duk wata ya yi masu kadan.

Majalisar NEC ta kungiyar likitocin ta yi wannan magana ne a lokacin da ta ke cikin yajin-aiki.

Jaridar ta rahoto NEC ta na cewa iyalan likitoci 19 da cutar COVID-19 ta kashe ba su iya karbar kudin inshora ba duk da alkawuran da gwamnati ta yi masu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here