Natasha: An yi sa-in-sa a Majalisar Dattawa

 

An yi sa-in-sa ne tsakanin ɗanmajalisan dattawa mai wakiltar Ebonyi ta arewa, Sanata, Onyekachi Nwebonyi da kuma tsohuwar ministar ilimi ta Najeriya, Oby Ezekwesili.

Lamarin ya faru ne a lokacin jin bahasin kwamitin ladabtarwa na majalisar dattijan, a zaman da ya yi don fara bincike kan zargin lalata da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi wa shugaban majalisar, Godswill Akpabio, a ranar Talata.

Sai dai a yayin jin bahasin sanata Onyekachi da tsohuwar ministar sun dinga zagin juna tare da nuna wa juna yatsa cikin fushi.

Ezekwesili ta halarci zaman jin bahasin ne tare da tawagar da ke ɓangaren Natasha. Yayin da sanata Onyekachi kuma shi ne mataimakin mai tsawatarwa na majalisar.

Amma daga bisani hankula sun kwanta, kuma kwamitin ya ci gaba da bincikensa.

Musayar kalaman dai ya ja hankali sosai a kafafen sada zumunta, kuma ya kasance ɗaya daga cikin manyan labaran da da ya mamaye kakafen watsa labarai na Najeriya a ranar Laraba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here