Yanzu dai babu batun zabe ko rantsar da zababbu. Sai nan da bayan shekaru hudu masu zuwa, idan Allah ya kaimu, an kuma kada kugen Siyasa, dan yin wani sabon zaben, a dukkan matakai na shugabanci. Allah yasa wadanda aka zaba kuma aka rantsar suyi abinda ya dace ga dukkan ‘yan Najeriya da ake wakilta ko ake Shugabanta.

Bayan kammala wannan zaben, da kuma rantsar da wadan da aka zaba, nayi nazarin abinda idona ya gani da abinda naji ko na karanta game da wannan zaben nan na 2019, mai dankaren tsada.

Abubuwa da yawa sun faru, mutane da dama sun shaida, ko da kuwa mutum bai je wajen zabe ba, to, ba zai kasa sanin abubuwan da suka gudana ba, ko a wajen yakin neman zabe ko a wajen zabe.

Tun daga batun yakin neman zabe da ‘yan takarkari suka yi a jam’iyyu daban daban, da shi kansa zaben, da kuma batun rantsar da wadan da aka zaba. Abubuwa masu dadi da marasa dadi sun auku.

Tabbatacce al’amari ne, tun lokacin da ake yakin neman zabe har zuwa lokacin zabe, an bayar da labarai na hasarar rayukan mutane da dama, musamman tsakanin magoya bayan ‘yan siyasa. Inda kusan galibin wadan da suka rasa rayukansu, a sanadiyar wannan zabe, talakawa ne, ko dai talaka aka kashe, ko kuma talaka ne yayi kisan.

Wato dai wadan da ake mulka sune suke kashe junansu, akan wadan da zasu mulke su. Su kuwa galibin wadan da ake wannan abu dan su, idan sun hadu da juna, musabiha suke yi, suna sakarwa juna fuska da murmushi, har ma a rungumi juna.

Idan kana jin musayar kalamai tsakanin wasu manyan ‘yan siyasa, ko ‘yan takarkaru, zaka yi zaton idan an hadu da juna, za a rabu dutse hannun riga, amma ina, sai kaga ana murna, ana murmushi, su kuwa magoya baya an barsu da cin mutuncin junansu da yiwa juna kallon hadarin kaji.

Babban abinda yafi jan hankali a wannan zaben, shi ne abinda kowa ya sani na yadda kudi suka taka muhimmiyar rawa a wannan zabe, kowa ya gani, yadda aka dinga sayen kuri’un mutane, suna yin zabe, babu batun cancanta ko ra’ayi, wanda duk yafi bada kudi mai kauri shi zai fi samun kuri’a.

To, babban tashin hankalin, shi ne, daga lokacin da talaka yace ba zai yi zabe ba sai an bashi kudi, to rannan ya sabbabawa kansa dawwama cikin talauci, a gefe guda kuma masu kudi da masu hannu da shuni zasu dawwama cikin daula da walwala.

Domin kuwa, shi talaka, shi da yin mulki haihata haihata. Saboda ba shi da kudin da zai rabawa masu zabe dan su zabe shi, danginsa ad abokansa ab su da kudin ad zasu taimaka masa, duk cancantarsa, duk kwarewa da gogewarsa, al’umma ba zasu zabe shi ba indai ba zai raba kudi ba.

Abin mamaki, kaga mutum, yana tare da mutane, sun sanshi, sun san dacewa da cancantarsa, amma idan bai basu kudi ba, ba zasu zabe shi ba, sun gwammace su zabi mara kirki fijiri, kawai dan ya raba musu kudi. Kaico!

Mai zai faru? Masu arziki da masu hannu da shuni zasu ci karensu babu babbaka, domin wanda duk jakar kudinsa tafi girma, tun a karon farko, shi ne zai samu tikitin tsayawa takara a cikin jam’iyya, kafin a tunkari babban zabe.

Muna sane, dukkanmu cewar, babu wani dan takara da zai samu tikitin tsayawa zabe a cikin kowacce jam’iyya sai ya sayi daliget, idan ma kato bayan kato ne, sai ya biya mutane kudi, sannan su hau layinsa, wannan abu ne da kowa ya sani.

Kafin dan takara ya shiga yakin neman zaben duk gari, zaka samu, ya kashe makudan kudade, balle kuma azo a tunkari babban zabe, inda nan ne ake madarar kashe kudi, banda kungiyoyi na coge da zasu yi ta kai bara wajen dan takara, zaka ga yadda ake kashe kudi kamar tsinko su ake daga bishiya.

Duk wannan ba komai yake nunawa ba, illa yadda rayuwar talaka ta shiga garari, kuma ya zama abin tausayi. A irin wannan yanayi wane talaka ne zai tsaya zabe yakai labari? Sai dai idan yana da ubangida hamshakin mai arziki da zai tsaya masa, alabashshi daga bisani shima a biya masa tasa bukatar.

Masu kudi zasu tallafawa ‘yan uwansu masu kudi dan suci zabe, saboda sune za a baiwa manyan manyan kwangiloli masu tsoka, bugu da kari kuma sune za a baiwa manyan mukamai na gwamnati wadan da ake samun kudade masu tsoka.

Kana tsammanin akwai wani talaka da zai tsaya zabe, masu kudi su taimaka masa da kudin shiga zabe, dan kawai ya cancanta? Idan wannan shi ne tunaninka, to, ka farka, dan mafarki kake yi, talaka ya sanya siyasar Najeriya ta sake yin tsada sosai.

Wadannan masu kudin, ba zasu taba damuwa da duk wani zagi da cin mutunci, da talakawa zasu yi musu, a kafafen sadarwa ko yada labarai ba, domin abinda suka kwana da saninsa, shi ne, talaka zai zabe su matukar sun bashi kudi a ranar zabe.

Wani zubin sai ka kasa fahimtar hakikanin hankali da tunanin mutane, kaji mutum ko ina zaginsa ake yi, ana ambaton rashin kirkinsa, amma ranar zabe idan yazo, ya bayar da kudi, kaga ana zabarsa ana murna, mutane da yawa zasu iya bada misalai akan haka.

A irin wannan tsarin demokaradiyyar jari hujja, kana zaton talaka zai fita daga wahala da talauci? Kana zaton zai dandana zakin kudi da dadin mulki? Dan talaka yayi karatun digiri ko NCE da kyar ya bige da samun jarin Naira dubu goma, ko aikin koyarwa a makarantun ‘ya ‘yan talakawa, shima na wucin gadi, bayan shekara biyu a sallame shi a dauki wani.

Akwai talakawa futuk da zasu iya samun mukamai, ko suci zabe, amma ‘by accident’, kamar yadda ya faru a jihar Zamfara, amma shima irin wannan din; za’a kawo karshensa, ta yadda masu hannu da shuni zasu yiwa talakawa tara tara, ta yadda komai kankantar jam’iyya, in kai talaka ne ba zaka iya yin takara a ciki ba.

Saboda sharuddans da za a gindaya maka, ba zaka iya shiga zabe a kila wa kala ba, ta yadda zaka gwammacekasa kudinka a inda idanma asara ce zata zo da sauki. A irin wannan tsari lokaci zai zo, hatta kananan mukamai da ake ganin jeka nayika ne, in ba kada kudi ba zaka taba jin kanshinsu ba.

Domin kuwa, su wadan da suke kan karagar mulki, wadan da suka shake jam’iyyu, ba zasu taba yadda ka shigo cikinsu kayi takara ba, sai sun tatseka kudi mai yawa, sannan ka iya samun damar tsayawa a matakin zaben fidda gwani.

Haka nan, lokaci zai zo, mukamin da zababbu suke bayarwa dan a tayasu aiki, shima sai mai kudin da zai iya basu, dan mayar da kudaden da suka kashe wajen yakin neman zabe, sannan zasu yadda su baka mukamin Kwamishina ko SA ko wani shugaban wata hukuma ko ma’aikata.

Duk wannan zai faru ne, sakamakon cewar da talaka yayi ba zai yi zabe ba, sai an bashi kudi. Matukar bamu tashi muka yi yaki da zuciyarmu ba, muka hakura da kadan din da za a bayar lokacin zabe, to tabbas zamu cigaba da zaman kashin dankali a Najeriya, hatta nana.

Idan kuwa mutane sun yiwa kansu kiyamul laili, to, sune zasu ci gajiyar jajircewa da tsayawa kan manufa ta zaben mutanan da suka dace, suci gajiyar ayyukan da suka dace, wadan da zasu kyautata rayuwarsu da ta yalansu.

Idan kuwa ba haka ba, to ba shakka, talaka zai dawwama a cikin talauci da wahala, masu kudi zasu dawwama a cikin daula da walwala. Allah ya kiyaye.

Yasir Ramadan Gwale
15-06-2019

The post Nazarina dangane da zaben 2019 – Yasir Gwale appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here