Ƙungiyar NBA ta yi Allah -Wadai da Kisan Alkali a Jihar Imo
Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta yi Allah wadai kan kisan da wasu ‘yan bindiga suka yi wa Nnaemeka Ugboma wani alƙali da ke jagorantar wata ƙaramar kotu a ƙaramar hukumar Oguta a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran ƙungiyar Akorede Habeeb Lawal, ya fitar ya ce ƙungiyar Lauyoyin ta tabbatar da kisan mista Ugboma ranar Juma’a da rana da wasu ‘yan bingiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi a harabar kotun da yake jagoranta.
Read Also:
Shaidun gani da ido sun ce alƙalin ya kammala wata shari’a kenan a daidai lokacin da maharan masu yawan gaske suka shiga cikin kotun inda suka karɓe wayoyin mutanen da ke cikin kotun, tare da kewaye alkalin daga bi sani kuma suka harbe shi da bingida.
Sanarwar ta ci gaba da cewa ”Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya NBA ta bayyana damuwarta kan kisan Nnaemeka Ugboma, wanda shi ne kisa na baya-bayan nan da ‘yan bindiga ke yi wa ma’aikatan shari’a da aƙalai a wani abu da ya zama mai matukar tayar da hankali a jihar Imo”
Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta ɗauki matakai domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar musamman ta hanyar girke jami’an tsaro masu yawa a harabar gine-ginen kotunan jihar.
Haka kuma NBA ta ce tana bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan kisa don gurfanar da su gaban kotun don su girbi abin da suka shuka.