NDLEA ta cafke Wasu Mutane da Miyagun ƙwayoyi

Hukumar NDLEA ta damke mutane 92 da take zargi da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Kano.

NDLEA ta samu wannan gagarumin nasara ne a cikin watan Oktoba.

Shugaban hukumar a Kano, Ibrahim Abdul, ya ce nauyin miyagun kwayoyin da aka kama a hannun mutun 92 din ya kai kilogram 987 Hukumar da ke kula da hana fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta ce ta kama wasu mutane 92 da ake zaton masu fataucin miyagun kwayoyi ne da kwayoyi da ya kai nauyin kilogram 987 a Kano cikin watan Oktoba.

Kwamandan hukumar a jihar, Dr Ibrahim Abdul, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a fadin birnin Kano, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya bayyana cewa farautar masu fataucin miyagun kwayoyin da hukumar ke yi bisa kudirin rage yawan fataucin kwayoyi da ta’ammali da shi a jihar na haifar da ‘ya’ya masu idanu.

“An gurfanar da mutum tara a gaban kotu, yayinda aka kai yan kwaya 101 bangaren gyaran hali, an tsare hudu, sai kuma biyu da aka sallama”, inji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here