Hukumar NDLEA ta Kama ‘Dan Bautar Kasa Dauke da Alawan da Aka yi da Miyagun Kwayoyi

 

Hukumar NDLEA ta kame alawan da aka yi da miyagun kwayoyi a babban birnin tarayya Abuja.

NDLEA ta ce an kame kayan ne yayin da aka gano an shigo dasu ne tun daga kasar Burtaniya.

Hakazalika, a wasu bangarori an kame wasu kayan laifin da za a fitar zuwa kasashen waje.

Abuja – Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta ce ta cafke wani dan bautar kasa mai shekaru 22, Arnold Maniru, bisa zargin shigo da kilo hudu na muggan kwayoyi daga Burtaniya, Punch ta rawaito.

Daraktan yada labarai na hukumar NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka bayar ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi 5 ga watan Satumba a Abuja.

Babafemi ya ce an kama dan bautar, wanda ke aiki tare da wata hukumar gwamnati a Abuja, a ranar Asabar, 28 ga watan Agusta, bayan da aka kame wani kaya a dakin ajiya na wani kamfanin sufuri.

Ya ce daga baya an aiwatar da isar da fakitin, wanda ke dauke da alawa da aka likawa alama da arizona an kuma samu wani babban nau’in tabar wiwi da migayun magunguna na ruwa.

Hakanan, jami’an da ke aiki da kamfanonin sufuri da sakonni a Legas sun kama kilo 1.2 na wiwi, wanda aka boye a cikin biskit da nufin fita dasu zuwa Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa.

Babafemi ya ce an kuma kame giram 920 na hodar Iblis da aka boye cikin gashin roba ake shirin tafiya dasu zuwa Saudi Arabiya daga jahar Legas.

Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), a ranar Alhamis 26 ga watan Agusta, ta karbi kayayyakin magunguna marasa rajista da darajarsu ta kai Naira miliyan 100 da Hukumar Kwastan ta kama.

Kwanturola a sashin B na sashin ayyukan kwastam na tarayya, Al-Bashir Hamisu ne ya mika kayayyakin ga NAFDAC a Kaduna, Daily Nigerian ta rawaito.

Mista Hamisu ya ce rukunin masu sintiri na kan iyakokin kwastam sun kwace kayayyakin magungunan ne a watan Agusta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here