Hukumar NDLEA ta Kama Hodar Iblis ta Hiroin da Nauyinta ya Kai 23.55kg
Hukumar yaki da masu ta’ammali da miyagun kwayoyi ta Najeriya ta ce ta kama hodar Iblis ta hiroin da nauyinta ya kai kilogram 23.55, wadda aka boye a cikin katan-katan na abincin jarirai.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, wanda ya bayyana labarin ya ce an kama hodar Iblis din ne, wadda kudinta ya kai sama da naira biliyan 4.5, kwatankwacin dala miliyan 10.8, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagos, bayan an shigo da ita kasar ta wani jirgin sama na Afirka ta Kudu daga birnin Johannesburg.
Read Also:
Jami’an hukumar sun ce an damke mutum uku da ake zargi da lamarin, wadanda suka hada da wasu ma’aikatan kamfanin dakon kaya da ainahin wanda zai karbi kayan, mai suna Chike Ikeke Eweni.
Haka kuma hukumar ta NDLEA, ta ce ta kama wani bireba, Muyiwa Babalola Bolujoko, wanda ya hadiyi kuli-kullin hodar koken guda 90.
Shi ma an kama shi ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammed din da ke Lagos, yayin da yake shirin tafiya Dubai ta jirgin sama na Qatar.
Kakakin hukumar, ya ce bayan da gwajin na’ura ya nuna musu cewa mutumin mai shekara 39, yana dauke da hodar a cikinsa ne, sai aka tsare shi, inda ya kasayar da dukkanin kullin 90.
Hukumar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike a kan dukkanin batutuwan biyu.