Fashi da Makami: Hukumar NDLEA ta Kama Mutane 8 a Legas

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun kama mutum takwas a wani kungurmin daji da ake zargi da aikata ta’addanci da garkuwa da mutane da kuma fashi da makami a dajin jihar Ondo.

An kuma samu abubuwa masu fashewa da bindiggi da harsasai da kuma tabar wiwi.

Wakilin BBc ya ruwaito cewa lamarin na zuwa ne a lokacin da hukumar ta kama wani mutum dan shekara 53 mai suna Ehiarimwiam Osaromo Emmanuel da kwayar Tramadol a zauren a filin jiragen sama na Murtala Muhammed dake a Legas.

A sanarwar da Femi Babafemi ya aike wa manema labarai ya ce jami’an hukumar ta NDLEA sun kaddamar da samamen ne bayan wani rahoto da aka tsegunta musu, sai suka fantsama cikin kungurmin dajin Ala da ke karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo, inda suka kama mutum takwas.d

An kama wadanda ake zargin ‘yan fashin ne a ranar Juma’a, 2 ga Satumba, 2022.

Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da buhu 25 na ganyen wiwi mai nauyin kilogiram 296, da wasu abubuwa masu fashewa kamar bom guda shida da harsashin bindiga shida.

Akwai kuma babura guda hudu da layu daban daban da suke amfani da su wajen aikata ta’addanci kan mutane da suka sha tsarewa a dajin.

Wannan na zuwa ne a lokacin da jami’an suka kama wasu mutane masu sarrafa hodar Ibilis da ake kira Metanpethamine a Agbara dake a wajen birnin Legas.

Kamen hodar methanpethamin ya zo a lokacin da jami’an hukumar suka sake kama wani mutum mai suna Ehiarimwiam Osaromo Emmanuel a zauren masu shirin tafiya a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke a Legas bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyi nau’in Tramadol kimanin kwali dubu biyar da ya boye a cikin jakarsa.

A Sokoto, jami’an tsaron NDLEA sun kama wata motar bas ta kasuwanci inda aka kwato na’urar kunna CD guda biyu da ke kan hanyar Sokoto zuwa Bodinga inda a gano tabar wiwi mai nauyin kilogiram 5.5 a cikin na’urorin, tare da kama mai kayan Nasiru Ibrahim, mai shekara 37.

Wata ‘yar kasuwa a Abuja mai suna Onyinye Nwoke mai shekaru 38, dubunta ya cika bayan jami’an leken asiri sun kai samame a gidanta da ke rukunin gidaje na Aldenco Estate, da tabar wiwi da aka noma a bayan gidan.

A jihar Neja, jami’an hukumar NDLEA a ranar Alhamis da ta gabata sun kama wata mota da ke jigilar dabbobi daga Legas zuwa Kaduna dauke da buhunan tabar wiwi a daskare har guda 449 da wasu buhunan 111 mai nauyin kilogiram 1,531 mallakin wani dila a Zaria.

An ce an yi lodin miyagun kwayoyi ne a cikin motar daga a Akure, ta jihar Ondo.

Direban babbar motan mai suna Yahaya Sani da mataimakinsa Samaila Rabiu da yaron motarsa Bilal Ibrahim da wakilin mai tabar wiwi, Auwalu Isyaku da fasinja Mustapha Abdulrahman duk an kama su.

A jihar Gombe, jami’an ‘yan sanda sun kama sinki-sinki na kwayar Tramadol, dubu dari takwas da sha daya da Diazepam da Exol 5, masu nauyin kilogiram 150 a cikin wata mota da aka yi mata lodi daga Onitsha na jihar Anambra.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here