Hukumar NDLEA ta Kama Mai Safarar Kwayoyi Wanda ya Hadiye Hodar Iblis ta kimanin N423m

 

Hukumar NDLEA ta yi babban kamu a tashar jirgin Murtala dake Legas.

Wannan karon, mutumin ya yi bahaya sau biyar inda ya kashe dukkan hodar da ya hadiya.

Masu safarar kwayoyi sun dade suna amfani da wannan hanyar wajen fita dasu daga Najeriya Jami’an hukumar dakile muggan kwayoyi watau NDLEA sun damke wani Henry Okonkwo bayan ya yi kokarin safarar hodar Iblis daga Najeriya zuwa kasar Andalus.

Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma’a.

A jawabin ya bayyana cewa an damke Okonkwo ne a tashar jirgin Murtala Mohammed dake Legas ranar Lahasi bayan ya yi kashin nadin hodar Iblis 113 da ya hadiya.

Femi Babafemi ya bayyana cewa farashin hodar Iblis da Okonkwo ya hadiya zai kai N423 million.

Ya ce Okonkwo ya yi niyyar kai hodar kasar waje ta jirgi yayinda aka damkeshi.

“Awanni 24 bayan tsareshi kuma ana sauraron yayi bahaya, mutumin wanda ya kwashe shekaru 10 a kasar Andalus ya yi kashin nadin hodar Iblis 39, sannan daga baya yayi ba hayan nadi 113,” jawabin yace.

“Karin bincike ya nuna cewa ya hadiyi wannan magani ne a dakin Otal dake Igando, jahar Legas.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here