Hukumar NDLEA ta ƙona Ganye Mai sa Maye Mai Nauyin kilogram 7,286

 

Gabanin babban zaɓen Najeriya na 2023 da ke tafe a ranar Asabar, jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta NDLEA, ta bayyana lalata ganye mai sa maye mai nauyin kilogiram 7,286 bayan yin dirar miƙiya a wani gandun dajin Ujiogba da ke jihar Edo.

A wata sanarwa da darektan yaɗa labaru na hukumar ya fitar a shafinta na twita, ya ce ta gudanar da samamen ne a ranar Laraba bayan samun bayanan sirri da ke cewa masu tu’ammali da kwayoyi sun shiga dajin rike da ɗaruruwan jakukkunan ganyen domin rarrabawa zuwa wasu jihohi gabanin gudanar da zaɓen.

NDLEA ta ce sai da jami’anta suka shafe tsawon lokaci suna artabu da ‘yan bindiga da kuma manya masu safarar ƙwayoyi kafin ta samu nasara a kansu, inda bayan nan ta cinna wuta kan wasu jakukkunan tabar wiwi da dama, tare kuma da tafiya da wasu guda bakwai domin gudanar da bincike da hukunta waɗanda ake zargi.

Ta kuma ce ta ƙwato bindiga ƙirar AK47 da wasu ƙananan bindigogi da kuma harsasai, inda suka kama wani ɗan shekara 24 mai suna Calvary Essien da ake zargi da tu’ammali da miyagun ƙwayoyin.

Da yake mayar da martani, shugaban hukumar, Birgediya-Janar Buba Marwa mai ritaya, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da samamen da kuma wasu kusan 10,000 da aka tura zuwa faɗin jihohi domin sa ido gabanin zaɓe wajen ganin ‘yan bangar siyasa basu yi amfani da ƙwayoyi ba kafin da lokaci da kuma bayan zaɓe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here