Hukumar NDLEA ta ƙwace ƙwayar Tramadol Sama da Miliyan 2.7 a Legas

 

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta kama ƙwayar Tramadol sama da miliyan biyu da dubu dari bakwai, da aka yi yunkurin fita da ita kasashen waje daga tashar ruwan Apapa da ke birnin Legas.

A sanarwar da NDLEA ta fitar jiya Lahadi, ta ce kwayar na dauke ne a cikin katan-katan 55, da suka hada da nau’ukan Tapentadol da kuma Carisoprodol na Tramadol, da kudinsu ya kai naira miliyan daya da dubu dari uku da saba’in da biyar.

Hakama NDLEA ta bayar da lambar kwantenar da: SUDU 7538656, inda ta ce ta samu bayanan sirri da suka tabbatar mata abin da ta ke dauke da shi.

Ko a makon da ya gabata an kama mutum biyar a tashar jirgin saman Murtala Muhammad da ke Ikeja a Legas din, yayin da suke yunkurin fitar da wasu nau’ukan kwaya zuwa biranen London da Dubai.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here