Jami’an Hukumar NDLEA Sun Lalata Tan 40 na Ganyen Tabar Wiwi

 

Jami’an hukumar hana sha ta fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami’anta sun lalata tan 40 na ganyen wiwi a jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Hukumar NDLEA ta kuma kama fiye da tan huɗu na muggan ƙwayoyi a lokacin samame daban-daban da suka ƙaddamar a jihohin Legas da Kogi da jigawa da Kaduna da Sokoto da Edo da kuma birnin tarayya Abuja a cikin makon da ya gabata.

Cikin sanarwar kame da hukumar ta fitar a shafinta na X da a baya aka fi sani da Twitter, ta ce a ranar 22 ga watan satumba ta kama tukwanen sinadarin ‘laughing gas da ake amfani da shi wajen kashe raɗadi don cire haƙori’ su kimanin 1,194 da nauyinsu ya kai kilogiram 2,547.2 da aka loda su cikin wasu motoci guda biyu a kan babbar hanyar Okene zuwa Lokoja zuwa Abuja.

Hukumar ta ce ta kama mutum biyu bisa zargin mallakar tukwanen wadanda ta ce suna yunƙurin safarsu zuwa Abuja daga jihar Kogi mai makwabtaka da Abujan..

Sanarwar NDLEA ta ce hukumar ta kama wata mata mai shekara 48, a wani samamen da ke da alaƙa da kamen, inda aka same ta da alluran pentazocine mai bugarwa 2,400 da ƙwayar exol 100,000.

Jami’an hukumar da ke Abuja sun kuma kama kilogiram 977 na sinƙin wiwi cikin wata babbar motar ɗaukar kaya da aka yi basajarta cikin kwalayen maggi.

Haka kuma jami’an na NDLEA sunce sun kama wata babbar mota ɗauke da sinƙin wiwi a jihar Ondo da ke kudu mso kudancin kasar.

Sannan kuma suka kama kilogiram 959 na tabar ta wiwi da aka so yin safararta zuwa jihar Sotoko.

A nan ma hukumar ta ce ta kama mutum biyu da take zargi na da hannu a safarar ƙwayar.

A ranar 23 ga watan satumba ma hukumar ta ce ta kama kilogiram 89.1 na sinkin tabar wiwi a kan hayar Kano zuwa Hadejia a jihar Jigawa a lkacin da jami’an hukumar ke binciken ababen hawa.

Hukumar ta kuma ce hukumar na gudanar da gangamin wayar da kan jama’a kan illar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ta hanyar shirya gabatar da jawabai na musamman a masallatai da makarantu da fadojin sarakunan gargajiya a jihohin kasar daban-daban.

Sanarwar ta ambato shugaban hukumar Burgediya Janar Buba Marwa mai ritaya na yaba wa jami’an hukumar na rassana jihohin da aka gudanar da kamen bisa manijin ƙokain daya ce sun yi a lokacin gudanar da ayyukansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com