Hukumar NDLEA ta kama Tsoho Mai Shekaru 70 da Yake Safarar Miyagun Kwayoyi

Hukumar NDLEA ta kame wani tsoho dake jigilar kai wa ‘yan ta’adda a Najeriya muggan kwayoyi.

Hukumar ta kuma dira wata katafariyar gonar taba a wani yankin jahar Ondo a kudancin kasar

Hakazalika ta samu nasarar kame wani bata-gari da harin taba a wani shingen ababen hawa a jahar Kogi

Hukumar hana sha da fatauncin miyagun kwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta bayyana cewa ta kwamushe wani tsoho dan shekara 70 da ake zargi dai kai wa ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram miyagun kwayoyi.

NDLEA ta ce tsohon na zuwa ne daga jahar Agadez ta Jamhuriyar Nijar inda daga nan yake shigo da kwayoyin cikin kasar ta Najeriya.

Cikin wata sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce, tsohon mai suna Muhammad Rabi’u Wada da ke kai wa Boko Haram da ‘yan bindiga kwaya an kame shi ne a jahar Neja kan hanyarsa ta komawa Jamhuriyar Nijar.

A wani samame da hukumar ta kai mai kama da wannan, ta samu nasarar lalata gonar tabar wiwi a jahar Ondo da ke kudancin Najeriya wadda girmanta ya kai kimanin hekta 95.

An samu gonar ne a wani dajin dake Ogbese, sai dai ba a samu nasarar kame kowa ba yayin samamen, amma ana ci gaba da bincike domin gano wanda ya mallaki gonar.

A jahar Kogi da ke arewacin kasar ta Najeriya, har ila yau Hukumar ta samu nasarar kwace tabar wiwi da ta kai kimanin kilogiram 116.1 a wani shingen ababan hawa a yankin Okene-Lokoja.

Mutumin da aka kama da kayan mai suna Sulaiman Said ya ce ya dauko tabar ta wiwi din ne daga jahar Edo a kudancin Najeriya kuma zai cilla da ita har zuwa Jahar Kaduna ne.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here