Gobara ta Tashi a Kusa da Masallacin Annabi Muhammad(SAW) a Birnin Madina

 

Gobara ta tashi a wasu gine-gine da ke kusa da masallacin Annabi Muhammad (SAW) a birnin Madina.

Shafin Haramain Sharifain ya ruwaito cewa an yi nasarar kashe gobarar cikin kankanin lokaci

Kawo yanzu hukumomi ba su bayyana abinda ya yi sanadin tashin gobarar ba ko abubuwan da aka rasa

Gobara ta tashi a wasu gine-gine da ke kusa da masallacin Annabi Muhammadu (SAW) a birnin Madina da ke kasar Saudiyya, kamar yadda shafin @hsharifain ya ruwaito.

Shafin Haramain Sharifain a Twitter ya wallafa wasu hotuna da bidiyon da ke nuna wasu gine-gine na ci da wuta tare da hayaki da ya turnuke saman ginin masallacin mai daraja.

Kawo yanzu ba a sanar da ainihin abinda ya yi sanadin tashin gobarar ba amma shafin na Haramain yace an yi nasarar kashe wutar nan take.

Ba a kuma bayyana abubuwan da suka kone sakamakon gobarar ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here