Gwamnatin Mulkin Sojin Nijar ta Bayar da Umurnin Fitar da Jakadan Faransa da ke ƙasar
Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta bayar da umurnin fitar da jakadan Faransa da ke ƙasar, inda ta ce a yanzu ya rasa kariyarsa ta diflomasiyya.
Read Also:
Mista Sylvain Itte ya ci gaba da zama a Nijar duk da cikar wa’adin sa’o’i 48 da aka ba shi na ya fice daga cikin ƙasar a ranar Juma’ar da ta gabata.
Sai dai gwamnatin Faransa ta bayyana cewa jakadanta a Nijar bai zai fice daga ƙasar ba saboda gwamnatin sojojin ba ta da hallaci.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar ta ce “muna nazari a tsaron lafiya da kuma kariya a ofishin jakadancinmu.”