Kungiyar NINAS ta Bayyana Cewa Zata Fito Zanga-Zanga a Ranar Juma’a a New York
Masu gangami karkashin inuwa wata kungiya, NINAS, sun ce babu gudu babu ja da baya, za su yi gangami a ranar Juma’a a UN.
Gangamin nasu zai yi daidai ne da ranar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi a taro na 76 na majalisar dinkin duniya.
Kungiyar ta zargi gwamnatin Najeriya da bai wa wasu bakaken Amurkawa kudi har $500 domin su fito nuna kaunar Buhari.
New York – Masu zanga-zanga tare da gangami karkashin inuwar kungiyar Nigerian Indigenous Nationalities Alliance for Self-Determination (NINAS), sun sha alwashin yin gagarumar zanga-zanga ta ‘yanci a hedkwatar majalisar dinkin duniya da ke New York a Amurka, ranar Juma’a.
Read Also:
Gagarumin gangamin da za su yi ya yi daidai da ranar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi a taron karo na 76 na majalisar dinkin duniya a ranar Juma’a, The Nation ta rawaito.
Akintoye a wata takarda ta ranar Alhamis da aka bai wa manema labarai, ya zargi gwamnatin tarayya da daukar nauyin wani zanga-zanga a hedkwatar majalisar dinkin duniya mai akasin hakan.
Ya zargi gwamnatin Najeriya da fara hayar bakaken fata da ke zama a Amurka inda aka biya kowanne mutum daya $500 domin zanga-zangar nuna goyon bayan Buhari da kuma fatan hadin kan Najeriya a hedkwatar majalisar dinkin duniya.
Akintoye ya sha alwashin cewa dole ne a fifita bukatar jama’a kuma sai sun fita zanga-zangar NINAS, The Nation ta rawaito.
Baya ga Akintoye, sakatare janar Tony Nnadi, wanda ya wakilci kungiyar sashin Niger da Farfesa Yusuf Turaki, wanda ya wakilci tsakiyar kasa nan a NINAS, sun hada kai tare da kira ga majalisar dinkin duniya da ta bada taimako wurin hana Najeriya fadawa rudu.