Hukumar NITDA ta Kammala ba da Horon Kwarewa ga Jami’an Gwamnati
Read Also:
A ƙoƙarin da ta ke cigaba da yi wajen horar da ƴan ƙasa, gami da bunƙasa ilimin jami’an gwamnatin tarayya kan amfani da fasahar zamani, hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa (NITDA), ƙarƙashin jagorancin Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar sadarwa da tattalin arziƙin fasahar zamani, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, (FNCS, FBCS, FIIM), ta kammala ba da horon bunƙasa ƙwarewa kan amfani da fasahar zamani ga jami’an gwamnatin tarayya.
Jami’an gwamnatin waɗanda su ka fito daga hukumomin tsaro da sauran sassan ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya, an ba su horon ƙwarewar akan harkokin tsaro na yanar gizo-gizo da sarrafa na’ura mai ƙwaƙwalwa.
Jim kaɗan da kammala horon a wannan rana, mai girma shugaban hukumar ta (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE) wanda Dakta Usman Gambo Abdullahi, shugaban sashen warware matsalolin ayyukan fasahar zamani na hukumar ya wakilta, ya miƙawa waɗanda aka horar ɗin takardunsu na shaidar samun horon, a cibiyar horar da ma’aikata da ke yankin Kubwa a birnin tarayya, Abuja.