Gwamnonin Arewa na APC Sun Gabatarwa Shugaba Buhari Sunayen Mutune 5 Daga Kudu Domin ba su Takara

Gwamonin Arewa na jam’iyyar APC sun gabatarwa shugaba Buhari sunayen mutane biyar da suke son a yi maslaha domin bai wa ɗaya daga cikinsu takara, a cewar jaridar Punch ta Najeriya.

Jaridar ta ce mutum biyar da gwamnonin suka gabatar da sunayensu duk ‘yan kudu ne da suka hada da tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da Kayode Fayemi na Ekiti da Rotimi Amaechi sai gwamnan Ebonyi, Dave Umahi.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan Filato, Simon Lalong, wanda ya tabbatar da wannan mataki nasu, ya ce sun gabatar da sunayen ne bayan dogon nazari da kuma tsallake tantacewa.

Sai dai gwamnan ya ce, wannan ba yana nufin za yi tasiri ko hana sauran masu nemana takara su shiga a fafata da su ba.

Ko a Jiya Litinin sai da gwamnonin suka yi ta ganawa da Shugaba Buhari domin cimma matsayar maslaha domin bai wa kudu takara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here