An Soma Tantace Daliget da za su Kaɗa kuri’a a Zaɓen Fidda Gwanin APC

 

An soma tantace daliget-daliget da za su kaɗa kuri’a a zaɓen fitar da gwani na neman tikitin takara a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Sama da daliget dubu biyu ne za a tantace domin zabo mutumin da zai fafata da ɗan takarar jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2023 da ke tafe.

Za a gudanar da zaɓen ne a dandalin Eagles square kuma kusan an kammala duk wasu shirye-shirye.

An tsaurara matakan tsaro, sannan an sauya fasalin wajen taron.

Mutum 23 ne suka nuna sha’awarsu ta takara a karkashin inuwar APC.

Fitattu a cikinsu akwai, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here