Mun Tsinci Bama-Bamai 3 da Basu Tashi ba a Cocin Katolikan Owo – Hukumar ‘Yan Sanda

 

Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa jami’anta sun tsince bama-bamai uku da basu tashi ba a Cocin Katolikan Owo.

A cewar Sifeton yan sanda, jami’ansa sun gano harsasan AK-47 a cikin cocin da aka kashe mutane.

Kwana biyu bayan kai harin, har yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin kuma ba’a san makasan ba.

Abuja – Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ta samu bama-bamai uku da basu tashi ba a cikin cocin Katolika dake garin Owo, jihar Ondo, Kudu maso yammacin Najeriya.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Kakakin hukumar yan sanda na kasa, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar.

A cewarsa, masu bincike sun tsince harsasai bindigar Ak-47 da aka yi amfani wajen hallaka rayukan masu bauta.

Yace:

“Bisa binciken da muka fara gudanarwa, yan bindigan sun kai hari cocin ne da makamai da bama-bamai.”

“Masu bincike na hukumar yan sanda na cikin wadanda suka fara dira wajen kuma sun ga harsasai AK-47 yayinda aka gano bama-bamai guda uku da basu samu tashi ba.”

“Yan bindigan sun gudu daga wajen cikin mota Nissan Sunny mai lamba AKR 895 AG wacce suka kwace hannun wani, kuma suka tsere ta titin Owo/Ute. An gano motar kuma mai ita na wajen yan sanda wajen bincike.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here